“Ba Zan Iya Auren Macen Da Ke Samun N5m Duk Wata Ba”: Matashi Ya Fadi Babban Dalili a Bidiyo

“Ba Zan Iya Auren Macen Da Ke Samun N5m Duk Wata Ba”: Matashi Ya Fadi Babban Dalili a Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan amsar da ya bayar kan tambayar "shin za ka iya auren macen da ke karbar miliyan N5 duk wata?"
  • Matashin ya amsa kai tsaye cewa ba zai iya ba, yana mai bayyana dalilinsa lamarin da ya zo wa mutane da dama a bazata
  • Yayin da yan mata da dama suka caccaki matashin kan amsar da ya bayar da dalilinsa, wasu sun goyi bayansa

Wani matashi dan Najeriya ya bayyana cewa ba zai iya auren macen da ke samun naira miliyan 5 duk wata a matsayin albashi ba.

Matashin ya bayar da amsar bazata a yayin da yake martani ga hirar na bidiyowanda wata matashiya ta gabatar kuma aka gano a TikTok.

Matashi yana jawabi
“Ba Zan Iya Auren Macen Da Ke Samun N5m Duk Wata Ba”: Matashi Ya Fadi Babban Dalili a Bidiyo Hoto: @dfet.tv
Asali: TikTok

Yayin da yake ba da amsa da a'a, mutumin ya bayyana cewa matar da ke karbar irin wadannan makudan kudi taka shi za ta yi.

Kara karanta wannan

“Soyayya Bata Tsufa”: Tsohuwa Mai Dogara Sanda Ta Amarce Da Sahibinta, Bidiyon Ya Yadu

Amsarsa a bidiyon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya, inda yan mata da dama suka caccake shi a matsayin mara wayo da rashin tunani.igerian-man-shares-strong-reason-t-marry-a-lady-earns-n5m-monthly-video-trends/

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai mazajen da suka jinjinawa amsar da ya bayar a matsayin mai tattare da hikima.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

user9006908979661 ya ce:

"Zan iya amma ba zan ketare iyakana ba kuma zan bari ta san cewa dudbu biyar dina daidai yake da miliyan 5 dinta."

Fboy Montana ya ce:

"Manta gayen nan na da wayo faaa."

Flair ta ce:

"Gayu mu dukufa kan addu'o'inmu sosai, mutanen kauyenmu basa so mu ci gaba."

chiboy? ya ce:

"Duba ga maganarsa yana da hujja.
"Wannan shine ra'ayinsa."

Morika Nadolistic ya ce:

"Dan uwa hikimarka ya fi gaban bayani, ka yi magana mai ma'ana, kimarka ya daga a wajena."

Kara karanta wannan

“Ta Gaji Da Auren Tun Ba a Kai Koina ba” Bidiyon Amarya Tana Kicin-Kicin Da Rai Yayin da Take Jerawa Da Angonta Ya Yadu

Yar tsohuwa ta yi wuff da sahibinta, bidiyon ya yadu

A wani lamari na daban, wata tsohuwa ta nunawa duniya lallai soyayya bata tsufa bayan ta shiga daga ciki da sahibinta a wani kayataccen biki.

Matar wacce ta hallara wajen bikin rike da sandar dogarawarta ta burge matasa da dama a dandalin TikTok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel