“Dole Aka Yi Mata?” Amarya Ta Yi Kicin-Kicin Da Fuska Yayin da Take Jerawa Da Angonta a Bidiyo

“Dole Aka Yi Mata?” Amarya Ta Yi Kicin-Kicin Da Fuska Yayin da Take Jerawa Da Angonta a Bidiyo

  • Wani bidiyo da ya yadu na wata amarya da ta yi murtuk da fuska yayin da suke taka rawa da mijinta ya haddasa cece-kuce
  • A ranar da ya kamata ya zamo mafi farin ciki a rayuwarta, matashiyar ta kasance cikin bakin ciki yayin da angon ke farin ciki
  • Mutane da dama da suka kallo bidiyon sun yi al’ajabin ko dai auren dole aka yi mata, yayin da abun ya ba wasu dariya

A wani al'amari da ya kamata ya zamo lokaci mafi farin ciki a rayuwarta, an gano wata sabuwar amarya cike da damuwa a tattare da ita.

Bidiyon ma'auratan suna jerawa yayin da manya da yara ke tayasu murna ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Amarya cikin bacin rai a wajen bikinta
“Dole Aka Yi Mata?” Amarya Ta Yi Kicin-Kicin Da Fuska Yayin da Take Jerawa Da Angonta a Bidiyo Hoto: @teiness
Asali: TikTok

Yayin da angon ke dauke da murmushi a fuskarsa sannan yana ta kokarin rike hannun amaryar don jerawa a tare, matashiyar ta yi kicin-kicin da fuska har aka gama.

Kara karanta wannan

“Suna Rayuwa Kamar Tagwaye” Matashi Ya Yada Bidiyon Kyawawan Matansa 2 Sanye Da Kaya Iri Guda

Ba a tabbatar da inda aka gudanar da auren da kuma ba a bayyana dalilin rashin farin cikinta ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon ya samu mutum fiye da miliyan biyar da suka kalle shi a TikTok kuma ya haifar da martani daban-daban.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a soshiyal midiya

user5581267770120 ya ce:

"Auren da aka yi shekarar nan cike suke da yaya Bernard."

user5824015152415 ya ce:

"Me ke damun ma'auratan nan, suna cikin tsananin bakin ciki. Allah Ubangiji ya kawo masu agaji."

favorahiantan ta ce:

"Abun da mutane da dama ke nema hummmmm ku yi farin ciki sannan ku yi godiya ga Allah kan wannan alfarma da ya yi maku."

keza Mulinda ya ce:

"Uuuuh ina ganin dole suka yi mata."

happiness ta ce:

"Shin wadannan mutanen biyu sun san abun da suke shirin shiga, don sun rigada sun gaji."

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

mayah19 ta ce:

"Mutane na ta aure sannan ga ni nan babu mai ganin goshina."

Matashi ya nunawa duniya tsala-tsalan mata biyu da ya mallaka a gidansa

A wani labarin, wani matashi da ke matukar alfahari da mallakan kyawawan matan aure har guda biyu ya garzaya soshiyal midiya don nunawa duniya su, ya ce tamkar tagwaye suke rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel