Malamin Kwaleji Ya Sha Jinjina Bayan Ya Dauki Jinjirin Dalibarsa Cike Da Sakin Fuska

Malamin Kwaleji Ya Sha Jinjina Bayan Ya Dauki Jinjirin Dalibarsa Cike Da Sakin Fuska

  • Wani lakcara ya sha ruwan yabo a dandalin TikTok bayan ya nunawa dalibarsa mace kauna
  • Kamar yadda aka gani a wani bidiyon TikTok da ya yadu, an gano malamin dauke da jinjirin dalibar tasa cike da farin cikin ganinsu
  • Mutane da dama sun yi martani ga bidiyon da kalamai masu ratsa zuciya suna masu bayyana malamin a matsayin mutum na daban

Wani lakcara da ba a san daga wani makaranta yake ba ya sha ruwan yabo da jinjina bayan wani bidiyonsa ya yadu a TikTok.

Malamin jami'a rike da jinjiri
Malamin Jami’a Ya Sha Jinjina Bayan Ya Taya Dalibarsa Rainon Jinjirinta Hoto: @Olashile75
Asali: TikTok

A wani bidiyo da ya yadu wanda @Olashile75 ya wallafa, an gano malamin dauke da jinjirin daya daga cikin dalibansa mata cike da farin cikin ganinsu.

A halin da ake ciki, bidiyon ya samu martani da dama daga masu amfani da TikTok. Kuma hakan ya taimaka wajen gano sunan makarantar da abun ya faru (LASPOTECH) wanda ke yankin Ikorodu na jihar Lagas.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gobara Ta Tashi Ana Tsaka Da Shagalin Bikin Aure, Jama'a Sun Ci Na Kare

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika da kallon bidiyon za a iya hasashen cewa malamin ya hadu da dalibar da jinjirin nata ne bayan wani dogon hutu.

Jama'a sun yi martani

@Miss wonderful ta ce:

"Ba lakcarorina ba, za su zage ka sannan su hada da danka."

@arin_wealth01 ta kuma yi martani:

"Kai daliban laspotech sun cika nan fa.....jijina ga daliban laspotian."

@christydam ta kuma ce:

"Gaskiya na ji dadin mutumin ya daukar mun yarona a lokacin gwaji hatta da jarrabawa harma ya ba shi kyautar kudi soyayya gareka yallabai."

@qweensammie ta ce:

"Malaman Laspotech sun kware a wannan faaaa kamar lakcarori 2 ne suka ba dana kudi suna da kirki da kula da yara."

@ashabiade364 ta tabbatar da yanayinsa tana mai cewa:

"Na san shi lakcaran psychology na a reshen isolo mutumin kirki."

@wuraolaherself20 ta bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Guntun Gatarinka Ya Fi Sari Ka Bani: Matashi Ya Gaji Da Biyan Kudin Haya, Ya Gina Daki 1 a Kan Filinsa a Bidiyo

"Ba a makaranta ta ba wasu lakcarorin ma cewa za su yi kada ka zo da yaro ajinsu ranar da na dauki yaron kawata na shiga korata aka yi waje sai ga malamin laspotech ya dauki yaron dalibarsa cike da farin ciki."

Dirarriyar budurwa da ta so yin aure a shekaru 22 ta fadi yadda rayuwa ta yi da ita

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa ta bayyana cewa ta so ace ta yi aure tana da shekaru 22 sannan ta haihu zuwa 25 amma Allah bai cika mata burinta ba har sai da ta kai shekaru 27.

Asali: Legit.ng

Online view pixel