Matashi Ya Kera Karamin Gida Mai Daki 1 a Filinsa, Ya Baje Kolin Yadda Aka Fara Aikin Har Zuwa Karshe

Matashi Ya Kera Karamin Gida Mai Daki 1 a Filinsa, Ya Baje Kolin Yadda Aka Fara Aikin Har Zuwa Karshe

  • Wani bidiyo da ke nuna gida mai daki daya da aka gina ya yadu kuma ya burge mutane da dama a soshiyal midiya
  • Mamallakin gidan ya ce ya yi aiki tukuru don gina muhallin nasa kuma cewa yana alfahari da cikar burinsa
  • Jama'a sun cika sashinsa na sharhi sannan suka rubuta masa sakonnin taya murna masu tsuma zuciya

Wani mutum mai suna @1issa_m, ya siye zukatan jama'a saboda gaskiyarsa game da yanayin rayuwa. Ya wallafa wani bidiyo da ke nuna gidansa mai daki daya, wanda ya gina tun daga tushe har sama.

Gida mai daki guda daya
Matashi Ya Kera Karamin Gida Mai Daki 1 a Filinsa, Ya Baje Kolin Yadda Aka Fara Aikin Har Zuwa Karshe Hoto: @1issa_m
Asali: UGC

Matashi ya wallafa nasarar da ya samu a TikTok

Mutumin ya bayyana a bidiyon cewa yana alfahari da hakan duk da cewar sauran mutane na iya yi wa gidan nasa kallon karamin daki.

Ya bayyana cewa har yanzu shi matashi ne kuma watakila ya mallaki babban gida da zai yi tinkaho da shi a nan gaba, don haka mutane na iya fadin abun da suke so.

Kara karanta wannan

“Sun Yi Kaman Uwa da ‘Da”: Bidiyon Shirgegiyar Mata Da Sahibinta Dan Tsurut Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun yi martani da dadadan kalamai a sashin sharhi sannan sun sake ba shi tabbacin cewa ginin dakin nasa babban nasara ne.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@user39472024061522 ya ce:

"Sannu da kokari dan uwa, shakka babu muhimmanabubuwa na zuwa sikubona ngalomsenzi umhle."

@Mashembu ya yi martani:

"Wuri da mutum zai kira gida."

@Cyndie ya ce:

"Sannu da kokari. Bulo nawa ka yi amfani da shi."

@xolisambobo ya rubuta:

"Sannu da kokari, wannan babban mataki ne ka dauka, Sannu da kokari."

@amandadebruin818 ya yi martani:

"Sannu da kokari danuwa."

Matashi ya kashe sama da miliyan N160 wajen siyar tsadaddiyar mota, an yi cece-kuce

A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi ya gwangwaje kansa da wata tsadaddiyar mota kirar Rolls Royce Cullinan wanda farashinsa ya kai kimanin naira miliyan 160 da yan kai.

Kara karanta wannan

Aljannar Duniya: Matashi Da Ke Biyan Miliyan N2 Kudin Haya Duk Shekara Ya Baje Kolin Gidansa a Bidiyo

Matashin wanda ya cika da alfahari ya baje koli tsaleliyar motar tasa a dandalin soshiyal midiya yayin da ya haska cikinta domin mutane su ba idonsu abinci.

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun taya shi murna yayin da wasu kuma suna nemi sanin wani irin aiki yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel