“Tinubu Ya Soke Tafiyarsa Zuwa Landan Da Saudiyya”: Inji Majiya

“Tinubu Ya Soke Tafiyarsa Zuwa Landan Da Saudiyya”: Inji Majiya

  • Babban jagoran jam'iyyar All Progressives Congress na kasa zai dawo Najeriya daga Paris a ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu
  • Wata majiya a cikin sansanin Bola Tinubu ta ce zababben shugaban kasar ya soke tafiyar da ya yi niyar yi zuwa Landan da Saudiyya
  • A cewar majiyar, Tinubu zai dawo ne don tattauna batun shugabancin majalisar tarayya ta 10 tare da zababbun yan majalisa

Zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu na iya dawowa kasar a ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu, yayin da fafutukar neman shugabancin majalisa ke kara zafi a tsakanin zababbun yan majalisar APC.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu mambobin sansanin Tinubu sun tabbatar da cewar tsohon gwamnan na jihar Lagas ya shirya dawowa daga Paris inda ya je hutawa sakamakon fafutukar neman shugabanci tsakanin zababbun yan majalisa.

Kara karanta wannan

Shin Za a Rantsar Da Tinubu a Matsayin Shugaban Najeriya a 29 Ga Watan Mayu? Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
“Tinubu Ya Soke Tafiyarsa Zuwa Landan Da Saudiyya”: Inji Majiya Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Wata majita ta bayyana cewa yayin da Tinubu zai dawo a ranar Litinin, don kammala tsare-tsaren bikin rantsar da shi wanda za ayi a ranar 29 ga watan Mayu, sannan a magance tashin hankalin da zababbun yan majalisa suka haifar.

Majiyar ta kuma bayyana cewa ta yiwu Tinubu ya soke tafiyarsa da ya shirya yi zuwa Landan da Saudiyya don yin Umrah sannan ya shirya dawowa Najeriya don magance wasu batutuwa na rabon manyan mukamai a majalisar tarayya ta 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Mun ji cewa Asiwaju ya soke tafiyarsa zuwa Umrah kuma yana iya dawowa Najeriya a ranar Litinin.
"Koda dai ba a fada mana dalili ba, ina zargin cewa baya rasa nasaba da yanayin da Kalu, Akpabio da Jibrin Barau suke ba hana APC bacci da kamfen dinsu na kamun kafa."

Za a rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, Babban Fasto

Kara karanta wannan

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani shahararren faston Najeriya kuma shugban cocin Evangelical Church of Yahweh Worldwide, Theophilus Olabayo, ya ce za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Malamin addinin ya ce duk da wasu na adawa da kasancewar hakan, Allah ya nuna masa cewa za a rantsar da Tinubu don zama shugaban kasa na gaba a watan gobe mai kamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel