Jirgin Sojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga a Birnin Gwari jihar Kaduna

Jirgin Sojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga a Birnin Gwari jihar Kaduna

  • Jirgin yakin rundunar sojin sama ya halaka yan bindiga da dama a wani kauye da ke yankin karamar hukumar Birnin Gwari, Kaduna
  • Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya ce sojoji sun samu rahoton yan bindiga sun shiga ƙauyen Sabon Layi
  • Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya yaba wa gwarazan Sojojin bisa kai ɗauki kan lokaci har suka samu nasara

Kaduna - Dakarun hukumar sojin sama na rundunar Operation Whirl Punch sun halaka 'yan bindigan jeji da yawa a wani luguden jirgin yaƙi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Kaduna.

Channels tv ta tattaro cewa 'yan bindigan sun kai farmaki ƙauyen Sabon Layi, yankin Birnin Gwari ranar Laraba kwatsam Sojoji suka far musu, suka sheƙa da dama.

Jirgin NAF.
Jirgin Sojin Sama Ya Halaka Yan Bindiga a Birnin Gwari jihar Kaduna Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce rundunar sojin sama ta kai ɗauki ne bayan samun kiran gaggawa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bene Mai Hawa 7 Ya Rushe, Ya Danne Danne Mutane da Yawa Ana Cikin Azumi

Aruwan ya yace yan bindigan sun bude wuta, suka tattara dabbobin jama'a da sace kyayyakin amfani da sauran muggan laifuka, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin gudun neman tsira.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nan take bayan haka, aka sanar da rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch kuma rahoto ya nuna ba tare da ɓata lokaci ba Sojojin suka kai ɗauki zuwa wurin.

"Yayin da suka isa wurin, Sojojin sun hangi 'yan bindiga tun a kusan nisan kilomita huɗu daga arewacin ƙauyen Sabon Layi, suna kokarin neman boye wa Jirgin yaƙi."
"Ana haka ne jirgin ya buɗe wa yan bindigan wuta kuma dakarun sojin sun sheƙe duk wanda suka bi ta kansa. Jirgin ya ɗauki lokaci yana shawagi a yankin kafin ya bar wurin."

- Samuel Aruwan

Kwamishinan ya kara da cewa gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya yaba wa jajirtattun Sojojin bisa kai ɗaukin gaggawa da nasarar da suka samu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Shiga Fada, Sun Yi Garkuwa da Basarake, An Bindige Wata Har Barzahu

Kaduna ta nemi karin kujerun hajji

A wani labarin kuma Kaduna Ta Nemi Karin Kujeru Daga Hukumar Jin Dadin Alhazai NAHCON

Hukumar jin daɗi da walwalar maniyyata ta jihar Kaduna ta ce zata nemi karin kujerun hajji 500 domin biyan bukatun wasu da ka iya cika ragowar kuɗinsu nan da yan kwanaki.

Shugaban hukumar ya yaba wa NAHCON bisa tabbatar da kuɗin kujera bai haura miliyan uku ba, ya faɗi manyan dalilan da yasa suka kara kuɗin aikin Hajji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel