Asiri Ya Tonu, Rundunar NSCDC Ta Cafke Wasu Manyan Motoci Makare Da Ma'adanai

Asiri Ya Tonu, Rundunar NSCDC Ta Cafke Wasu Manyan Motoci Makare Da Ma'adanai

  • Rundunar tsaro ta NSCDC ta samu nasarar kama wasu manyan motoci maƙare da duwatsu masu daraja a Zamfara
  • Rundunar ta cafke motocin ne yayin da suke ƙoƙarin barin cikin babban birnin jihar, Gusau, domin zuwa Sokoto
  • Kwamandan rundunar ya yi ƙarin haske kan kama motocin inda ya lissafo dalilan da ya sanya aka kama motocin

Jihar Zamfara- Rundunar jami'an tsaron Nigeria Security and Civil Defense Corps (NSCDC) ta jihar Zamfara ta kama wasu manyan motoci ɗauke da duwatsu masu daraja.

Kwamandan rundunar, Muhammed Muazu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Litinin a birnin Gusau.

An kama manyan motoci dauke da ma'adanai
Kyawawan duwatsu masu daraja Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ambato kwamandan na cewa motocin waɗanda ke maƙare da duwatsun an kama su ne a Gusau akan hanyar su ta zuwa Sokoto, inda ya ce direbobin basu da cikakkun takardu.

Kara karanta wannan

Ta Tabbata: 'Yan Bindiga Sun Ɗana wa Jami'an Tsaro Tarko, Sun Bude Musu Wuta

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ba mu da matsala da direbobin ko motocin, sai dai masu duwatsun su kawo mana cikakkun shaidu da suka ba su hurumin yin wannan kasuwancin.”

A cewar sa duk wani mutum ko kamfani da yake harkar ma'adanai, dole ne ya cika waɗannan sharuɗɗan:

Lasisin siye da siyar da ma'adanai, shaidar biyan kuɗin mallaka, sunan ma'adanin idan daga halastaccen waje yake, lasisin zirga-zirga da satifiket na wajen siyan ma'adanin.

Muazu ya baygana cewa idan har ba a kawo waɗannnan takardun ba, direbobi da duk wani mai hannu a ciki za su fuskanci hukunci, sannan za a riƙe motar da duk kayan da ke cikin ta kamar yadda doka ta yi tanadi, cewar rahoton Daily Post.

Ya ja kunnen direbobi

Ya cigaba da cewa motocin da aka kama direbobin su, suna da wa'adin kwana 7 su kawo takardun da ake buƙata ko kuma su fuskanci tuhuma.

Kara karanta wannan

Tahajjud: An haramtawa Limamai karanta Qur'ani ta waya a sallolin watan Ramadana

Kwamandan ya kuma gargadi direbobin manyan motoci da su dai na ɗaukar duk wani ma'adani har sai mai kayan ya kawo musu halastattun takardu.

NSCDC Sun Damke Wasu Masu Buga Nairori da Dalolin Karya

A wani labarin na daban kuma, hukumar NSCDC ta samu nasarar yin caraf da wasu ɓata gari buga dalolin bogi a jihar Zamfara.

Ɓata garin ba a iya buga dalolin bogi kawai suka tsaya ba, har sabbin takardun kuɗin naira suka bugawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel