Kwastomomin Banki da Ke Tura Sakon Korafi Sun Sumar da Imel Din Babban Bankin CBN

Kwastomomin Banki da Ke Tura Sakon Korafi Sun Sumar da Imel Din Babban Bankin CBN

  • Akwatin imel na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya daina karbar sabbin sakwanni saboda cikar da ya yi makil
  • Wannan ya faru ne tsabar da yadda kwastomomi ke tura sakon korafi ga CBN game da matsalolinsu da bankunansu
  • Kwastomomi da yawa na bankuna a kasar nan sun gaza samun mafita daga bankunansu, sun tafi neman taimako wajen CBN

Sashen kula da korafin kwastomomi na CBN mai adireshin imel cpd@cbn.gov.ng ya cika makil da tarin korafe-korafe daga kwastomomi.

Duk da ana tsammanin CPD ya iya magance matsalolin kudi na kwastomomin bankuna, amma alamu sun nuna matsalar na ci gaba da ci kamar wuta da daji.

Korafe-korafen mutane dai ya fara daga matsalar cire kudi ta ATM, cire musu kudi ba tare da ka’ida ba da kuma wadanda suka tura kudi basu shiga ba.

Kara karanta wannan

Madallah: Wata kungiya ta rabawa talakawa 750 kayan abinci a wata jihar Arewa

Akwatin imel din CBN ya cika
Yadda imel din CBN ya cika da sakwannin jama'a | Hoto: @cbn
Asali: Facebook

Ka’idar tura wa CBN korafi

Ana shawartar kwastomomin bankuna cewa, idan suka gaza samun hanyar warware matsala a bankunansu, su tura sakon korafi ga CBN ta akwatin imel din CPD.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ka’idojin da CBN ta sanya na turo mata korafi su ne:

  1. Sa’o’i 72 kan korafi game da cire kudi ta katin ATM ko kuma aka yi tiransfa
  2. Kwanaki 14 game da korafin da ya shafe kula da asusun banki
  3. Kwanaki 30 na cire kudi a asusun kwastoma da suka wuce misali

A baya, Legit.ng ta tattaro muku yadda mutum zai mika sakon korafi ga CBN idan ya gaza samun mafita daga bankinsa.

Sauyin kudi a Najeriya na daya daga cikin abubuwan da suka jawo matsaloli ga kwastomomi da masu mu’amala da bankuna a fadin kasar nan.

Hakazalika, karancin sabbin kudi da kuma yawaitar bukatuwa ga amfani da hanyoyi tura kudi daga asusu zuwa asusu ya sake sanya bankuna shiga matsi.

Kara karanta wannan

Ahaf: Gwamnatin Buhari ta gano kasashen Turai na daukar nauyin ta'addanci, sun sha suka

Dalilin da yasa CBN ya kirkiri manhajar eNaira

A wani labarin kuma, kun ji yadda babban bankin CBN ya bayyana manufar kirkirar manhajar musayar kudi ta eNaira.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan kasar ke fama da karancin sabbin takardun kudi da aka sauya a shekarar da ta gabata.

‘Yan Najeriya sun sha fama game da karancin kudi da kuma sauyin takardun kudi, kotu ta raba gardama game da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel