CBN Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin da Yasa Ya Kirkiri Manhajar eNaira da Kuma Tasirinta

CBN Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin da Yasa Ya Kirkiri Manhajar eNaira da Kuma Tasirinta

  • Har ila yau, CBN ya sake jaddada manufar kirkirar eNaira yayin da kasa ke ci gaba da fuskantar karancin sabbin kudi
  • An kaddamar da eNaira ne a watan Oktoban 2021, kuma gwamnati ta ce yinsa zai kawo sauyi a tsare-tsaren CBN na takaita amfani da takardun kudi
  • Yayin da karancin Naira da matsalolin sauya fasalin kudi ke ta'azzara, ‘yan Najeriya na ci gaba dasa ayar tambaya game da fa’idar eNaira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi karin haske game da eNaira da ya kaddamar, inda yace an yi sa ne don takaita kashe tsabar kudi da kuma rungumar hada-hadar kudi ta yanar gizo.

Samuel Giwa, mukaddashin manajan CBN na Akure ne ya ba da wannan bayanin a lokacin da ya ziyarci fadar Deji na lardin Akure, Oba Aladetoyinbo Adedelusi.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Da alamu an kusa daina ganin tsabar kudi, CBN zai iya kakaba wata hanyar biya

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Giwa ya ziyarci fadar ne domin neman goyon bayan jama’ar Ondo wajen amfani da manhajar eNaira a hada-hadarsu ta yau da kullum.

Dalilin da yasa muka kirkiri eNaira, inji CBN
CBN ya kirkiri eNaira don saukaka hada-hadar kudi a Najeriya | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Amfanin manhajar eNaira

Da yake jawabi ga jama’a, Giwa ya ce, eNaira zai habaka wa ‘yan Najeriya hanyoyin musayar kudade, zai rage rashawa da damfara kana ya kara fadada harkar hada-hadar kudi ga ‘yan kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa, eNaira ba wai kudi bane kawai ba, wata hanya ce ta kirkirar damammaki na musayar kudi da kuma saukaka hanyoyin hada-hada ga ‘yan kasar cikin sauki da tsaro.

A cewarsa:

“Babu shakka tsarin eNaira ya zama wani muhimmin ginshiki na tsarin hada-hadar kudi a Najeriya da kuma samar da wata hanya ta daban wajen hada-hada.
“Ba wai kawai za ta habaka tattalin arzikin Ondo bane, za ta habaka tattalin arzikin Najeriya baki daya; alamar ci gaba da kirkira ce, kuma za ta saukaka hanyar hada-hada cikin tsanaki da sauki.”

Kara karanta wannan

Yadda Aka Min Tayin N100m Don In Janye Takara, Dan Shekaru 33 Da Ya Kayar Da Kakakin Majalisar Yobe

Hakazalika, ya yi karin haske da cewa, eNaira zai taimaka wajen rage radadin da ake fama dashi na karancin sabbin kudi, don haka ya shawari al’ummar jihar ta Ondo da su gaggauta sauke manhajar, rahoton Vanguard.

Basaraken ya godewa CBN bisa wannan jawabin tare da kira ga al'umma da su rungumi sauyin da aka samu.

Za a kakaba amfani da eNaira

A wani rahoton, majiya ta bayyana yiwuwar CBN ya kakaba amfani da eNaira ga ‘yan Najeriya a halin da ake ciki.

Wannan ya biyo bayan karancin sabbin Naira da ake fama dashi a kasar da kuma yadda ‘yan kasar ke kokawa.

Har yanzu, ana ci gaba da kashe tsoffin takardun Naira saboda karancin sabbi da ake gani a bankunan kasar ga kuma kunci da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel