NDLEA Ta Kame Dan Kasar Waje da Ya Shigo da Hodar Iblis Zuwa Najeriya

NDLEA Ta Kame Dan Kasar Waje da Ya Shigo da Hodar Iblis Zuwa Najeriya

  • Hukumar NDLEA ta yi nasarar kwamushe wani matashi dan kasar Suriname da laifin shigo da hodar iblis cikin Najeriya
  • Rahoto ya bayyana yadda mutumin ya shigo Najeriya domin neman mahaifinsa da ya jima da bata mai suna Omini
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano gaskiyar dalilin shigowarsa da kuma yiwuwar daukar mataki a kansa

FCT, Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kwamushe wani matashi mai shekaru 34 da Kudancin Amurka daga yankin Suriname mai suna Dadda Lorenzo Harvy Albert bisa zarginsa da safarar miyagn kwayoyi.

Daraktan NDELA kan yada labarai, Mr Femi Babafemi ne ya bayyana kamun a ranar Lahadi 9 Afirilu, 2023 a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Babafemi ya ce, an kama mutumin ne a filin saukan jirage na Fatakwal a jihar Ribas a lokacin da ya shigo Najeriya da daurin hodar iblis 117.

Kara karanta wannan

"Dimukradiyya Ce Tsari Mafi Dacewa", Buhari Ya Fada Wa Jakadu A Sakon Bankwana

Yadda aka kama matashi da kayan maye a Fatakwal
Dadda Albert kenan, wanda ya shigoda hodar iblis a cikin kwaroron roba | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A cewarsa, matashin ya daure hodar ne a cikin kwarorin roba da ya boye a cikin kananan kwalaben turare.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda mutumin ya shigo Najeriya

Ya kuma bayyana cewa, mutumin ya yi ikrarin cewa, ya bar kasarsa ta Suriname da ke Arewa maso Gabashin Kudancin Amurka a ranar 2 ga watan Afrilu zuwa Sao Paulo da ke Brazil.

Daga nan, ya tsallako Najeriya daga Sao Paulo a ranar Juma’a 7 ga watan Afrilu ta wani jirgin kasar waje na Qatar Airways domin neman mahaifinsa dan Najeriya da ya jima da bata mai suna Omini, rahoton Punch.

Ya zuwa yanzu dai hukumar na ci gaba da bincike don gano gaskiyar lamari kafin daga bisani ta dauki matakin da ya dace kan safarar miyagun kwayoyi kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

An kama wasu matasa 7 a Bauchi da kwaya

A wani labarin, kun ji yadda ‘yan sanda a jihar Bauchi suka kame wasu matasa bakwai da ake zargin ‘yan Sara Suka ne da suka addabi mazauna.

An kama matasan dauke da kayayyakin bugarwa da kuma muggan makamai da ka iya kai wa ga halaka mutane.

Ya zuwa yanzu, an ce za a gurfanar dasu a gana kotu bisa laifin tayar da hankalin jama’a da kuma aikata laifin da ya saba doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel