Rikici a APC Yayin da Aka Kori Minista, Tsohon Gwamna da Jiga-Jigai da Yawa a Jihar Enugu

Rikici a APC Yayin da Aka Kori Minista, Tsohon Gwamna da Jiga-Jigai da Yawa a Jihar Enugu

  • Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Enugu bisa zarginsa da cin dunduniyar jam’iyyar
  • Hakazalika, an dakatar da minista Nnamani da sauran jiga-jigan jam’iyyar ta APC da ke jihar ta Enugu
  • Ya zuwa yanzu, an ce manyan jiga-jigan APC na Enugu sun hada baki wajen cin dunduniyar jam’iyyar a zaben bana

Jihar Enugu - Sashen jam’iyyar APC a jihar Enugu ta korar tsohon gwamnan jihar Enugu, Barr. Sullivan Chime da kuma daraktan gidan labarai na Voice of Nigeria, Mr Osita Okechukwu.

Hakazalika, jam’iyyar ta kuma kori tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Eugene Odo, hadimin ministan harkokin waje, Mr Flavour Eze da kuma Mr. Joe Mnamel da Mr Maduka Arum.

Hakazalika, jam’iyyar ta APC ta kuma dakatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani da kuma ministan harkokin wajen Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama.

Kara karanta wannan

An Bude Kofar Rikici, APC ta Kori Mataimakin Shugaban Majalisa da Tsohuwar Hadimar Buhari

Yadda aka kori jiga-jigan APC a Enugu
Jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Batun dakatar da wadannan ‘yan siyasan na fitowa ne daga bakin Mr. Robert Ngwu a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis 6 Afirilu, 2023, Tribune Online ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta bayyana cewa, ana zargin jiga-jigan na APC da cin dunduniyar jam’iyyar ta APC a zabukan da suka gabata.

A cewar sakataren, dakatarwar na zuwa ne bayan shawarwari da kuma duba cikin tsanaki na kwamitin ladabtarwa na APC.

An zarge su da goyon bayan ‘yan takarar wasu jam’iyyun siyasa da ba na su babban zaben 2023 da aka kammala a kwanakin baya.

Zaben shugaban kasa da na gwamnoni a bana ya zo da salo mai daukar hankali, lamarin da ya jawo cece-kuce tsakanin jam’iyyun siyasa daban-daban, Sahara Reporters ta ruwaito.

Peter Obi ya yi martani kan batun cewa ya ce siyasar bana ta addini ce

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Miyagun Yan Daba Sun Kusa Sheƙe Ɗan Takarar Gwamnan APC a 2023

A wani labarin, kunji yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi yace ana kokarin ganin ya bar Najeriya saboda wasu dalilai na siyasa.

Peter Obi ya ce, ‘yan APC na kitsa yadda za su bata masa suna da kuma kakaba masa laifin da bai aikata ba, inda yace hakan ba zai hana shi tabbatar da ya kwaci hakkinsa daga hannun APC ba.

Rahoto ya bayyana a baya cewa, Obi ya ce bai amince da sakamakon zaben shugaban kasa ba, zai nemi shigar kotu a lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel