Fathia Balogun, Mercy Aigbe Da Wasu Jaruman Nollywood 5 Da Suka Musulunta

Fathia Balogun, Mercy Aigbe Da Wasu Jaruman Nollywood 5 Da Suka Musulunta

Ana yawan samun sauye-sauyen addini tsakanin al'umma saboda wasu dalilai da suka hada da aure, ra'ayi, sha'awa da dai sauransu.

A cikin yan shekaru da suka shide, an samu wasu daga cikin jarumar fina-finan kudu wato Nollywood da suka karbi addinin musulunci saboda wasu dalilai nasu.

Wasu daga cikin jaruman da suka musulunta
Fathia Balogun, Mercy Aigbe Da Wasu Jaruman Nollywood 5 Da Suka Musulunta Hoto: Flor Media
Asali: UGC

A wannan zauren, Legit.ng ta kawo maku wasu jaruman Nollywood bakwai da suka musulunta. Ga su kamar haka:

1. Fatiha Balogun

Shahararriyar jarumar Nollywood, Fathia Balogun ta kasance kirista amma ta musulunta don auren tsohon mijinta, Saheed Balogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyayenta sun kasance yan darikar Katolika, ta fito daga kabilar Urhobo a Warri, jihar Delta.

Aurenta da Saheed shine yasa ta samu sunan Musulunci ‘Fathia’. Tana rike da mukamin Musulunci na ‘Atesin Se Addini’.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

2. Lola Alao

Jaruma Lola Alao ta girgiza intanet a 2016 lokacin da ta sanar da shigarta Musulunci da sabon sunanta ‘Rhodiat’.

Da take tabbatar da matsayinta, ta yarda cewa asalinta Musulma ce kuma cewa addinin ba sabon abu bane a gareta.

3. Lizzy Anjorin

Jaruma Lizzy Anjorin ta taso ne a gidan kirista, amma sai ta samu nutsuwa a Musulunci wanda shine addinin mahaifiyarta a 2013. Tana da sunan Musulunci guda biyu Sekinat da Aishat.

Ta bayyana a shafinta na Instagram a watan Janairun 2018 cewa ta yanke shawarar ne lokacin da mahaifiyarta ya rasu amma ba saboda namiji ba.

4. Laide Bakare

Jaruma Laide Bakare ta kasance kirista har sai bayan da ta rabu da kiristan mijinta sannan ta fara soyayya da Alhaji Tunde Orilowo.

Bayan ta aure shi sai uwar yara ukun ta karbi addinin Musulunci.

5. Adunni Ade

Jaruma Aduni Ade ta ba mutane mamaki a 2020 lokacin da ta bayyana cewa ita din Musulma ce yanzu. Sai dai, uwar yara biyun ta ce ta taso a cikin Musulunci amma mahaifinta ya ba ta damar yin duk addinin da yake so.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Dawo Ɗanye, APC Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Da Wani Babban Jigo

Ta kuma jaddada cewa ta fi samun nutsuwa da farin ciki a Musulunci.

6. Liz Da Silva

Bayan ta haifawa wani Musulmi da a 2013, jaruma Liz da Silva wacce haifaffiyar yar Togo ce ta musulunta sannan sunanta ya koma Aishat Olaoye.

7. Mercy Aigbe

Jarumar da ta karbi addinin Musulunci a baya-bayan nan a masana'antar ita ce Mercy Aigbe.

Mercy wacce haifaffiyar yar Edo ce ta bayyana cewa ta musulunta a kwanan nan lokacin da bidiyonta tana bayyana Sanin ta na Musulunci ya yadu. Yanzu sunanta Hajiya Meenah Mercy Adeoti.

Wannan bai zo wa mutane da mamaki ba saboda aurenta da Kazeem Adeoti wanda yake Musulmi ne.

A baya mun kawo cewa Mercy ta koka kan yadda rayuwarta ke tafiya a matsayin matar musulmi musamman a wannan wata na Ramadana.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel