Matsafa Sun Kashe Wani Matashi Malamin Addinin Islama a Hanyarsa Ta Zuwa Buda Baki

Matsafa Sun Kashe Wani Matashi Malamin Addinin Islama a Hanyarsa Ta Zuwa Buda Baki

  • Wasu tsagerun matsafa sun hallaka wani matashi malamin addini a wani yankin jihar Ekiti da ke Kudu masu Yamma
  • Rahoto ya bayyana cewa, matashin yana kan hanyarsa ta dawowa gida ne a lokacin da aka farmake shi, aka sheke shi
  • Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda basu tabbatar da faruwar lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton

Jihar Ekiti - Wasu ‘yan daba matsafa sun kashe wani matashi mai suna Ajagbe a yankin Ado Ekiti a jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya.

Majiyar jaridar Leadership ta tattaro cewa, matashin Musulmi ne kuma an farmake shi ne a yankin Atundaolu-Irona da ke jihar a ranar Litinin.

An farmaki matashin ne da aka ce malami ne na addinin Islama a lokacin da yake hanyarsa ta komawa gida sadda ya biyo yankin.

Kara karanta wannan

To fah: Matukin jirgi ya shiga tasku, maciji ya makale a kujerarsa sadda yake tuki a sama

Yadda aka kashe matashi malamin addinin Islama a Ekiti
Jihar Ekiti da ke Kudu mao Yammacin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru da yamma

An kuma ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun harbi mutumin, amma da suka ga bindigar ta ki shiga sai suka fasa kansa da dutse.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar kusa a yankin ta bayyana cewa, an san matashin da kame kai, kuma ba mai son tashin hankali da hayaniya bane.

Hakazalika, majiyar ta bayyana cewa, an kashe wani mutum mai suna Obo kafin kisan matashin, wanda aka ce tsagerun matsafan sun kashe malamin ne don daukar fansa.

A cewar majiyar:

“Alfa na kan hanyar dawowa gida kusan karfe 6:30 zuwa 7 na yamma don yin buda baki a sai matsafan suka farmake shi a yankin Atundaolu, kusa da gidan badala da ke hanyar Irona.”

‘Yan sanda basu tabbatar da faruwar lamarin ba

A lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ya ce zai tuntubi manema labarai game da lamarin nan ba da jimawa ba, The Hope Newspaper ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kame tsagerun 'yan bindiga 2 da suka addabi jihohin Arewa

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin na ‘yan sanda bai yi magana ba, bai kuma tabbatar da faruwar lamarin ba.

An kama wani mutumin da ke hako kabari

A wani labarin kuma, an kama wani mutumin da ke bin dare yana tone kaburbura dominsa ce kokon kan mamata.

An ruwaito cewa, an kama mutumin ne a lokacin da yake kokarin aikata mummunan aikin da ya saba doka.

Ya zuwa yanzu, an mika shi ga ‘yan sanda kafin daga bisani za a gurfanar dashi a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel