Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

  • Wani bidiyo na jarumar Nollywood, Mercy Aigbe tana mai sake gabatar da kanta a sabon addininta ya yadu
  • An yi hira da ita ne a wani taron Ramadan da jarumar ta shirya tare da mijinta wanda ya samu halartan manyan jarumai
  • Bidiyon wanda tuni ya yadu ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya

Mercy Aigbe ta sa masu amfani da soshiyal midiya yamutsa gashin baki bayan bayyanan wani bidiyonta da ya yadu.

Ku tuna cewa jarumar da mijinta, Adekaz sun gayyaci abokai, abokan sana'a da yan uwa zuwa taron Ramadan.

Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta
Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci Hoto: @therealmercyaigbe, @thetattleroomng
Asali: Instagram

Bayan nasarar da ta samu a taron, an yi hira da jarumar inda ta tabbatar da cewar ta bar addinin kirista zuwa na Musulunci.

A bidiyon, an iya gano jarumar tana sake gabatar da kanta da sunayenta da suka hada da na Musulunci.

Kara karanta wannan

Kaico: An debi 'yan kallo yayin da saurayi ya kama budurwa a otal tana karuwanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamanta:

"Sabon sunana shine Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

mz__seunfunmi:

"Wannan bai dameni ba sunan da na san ki da shi shine mercy aigbe."

openspeaker_1:

"Idan suka rabu daga baya fa??? Kada ta je ta bi boka faaaa."

benny_lee04:

"Soyayya na shirin gamawa da mercy."

official__jessie:

"Muna nan gaba daya lokacin da idanun mutumin nan za su bude."

ladyrealtorzinnie:

"Ina fatan ba za a ji labari daban ba anjima idan sabuwar mata ta shiga saboda...."

l.tobiloba:

"Ban taba ganin barauniya mai alfahari ba. Ina fatan za ki ci gaba da wannan karfin halin idan sabuwar mata ta shigo."

i_am_nova_kae:

"Za ka yi tunanin wasu matan za su fi hikima amma soyayya sa'anka ne?"

david_chibuzo_690:

"A kan mijin wata."

Mata na kokari da Ramadana, Jarumar fim ta koka

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 8, Matashiya Ta Haifi Yara Biyar, Maza 3 Da Mata 2, Bidiyon Ya Yadu

A gefe guda, mun kawo a baya cewa jarumar fim, Mercy Aigbe ta koka kan yadda rayuwarta ke tafiya a matsayin matar musulmi musamman a wannan wata na Ramadana.

Mercy ta ce ta fara sabawa da azumin Ramadana amma babban kalubalanta shine tashin asubahi don shirya sahur domin a cewarta sam bacci baya isarta kuma hakan kan sa duk sai ta ji ta gaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel