Matashi A Kano Ya Yi Ajalin Budurwarsa Yar Shekara 22 Mai Juna Biyu Ta Hanyar Shake Wa

Matashi A Kano Ya Yi Ajalin Budurwarsa Yar Shekara 22 Mai Juna Biyu Ta Hanyar Shake Wa

  • Philibus Ibrahim, wani mutum a Kano ya shiga hannun yan sanda kan zargin sanadin ajalin budurwarsa yar shekara 22 mai dauke da juna biyu
  • Wani dan kasa na gari ne ya gano buduwarsa kwance a gefen titi ba ta numfashi ya kuma ankarar da hukuma aka taho aka kai ta asibiti, likita ya tabbatar ta riga mu gidan gaskiya
  • Wanda ake zargin, Ibrahim, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa an kuma kama abokin harkalarsa, Gabriel Bila, dukkansu na zaune a Unguwar Koraru a T/Wadan Kano

Jihar Kano - Jami'an yan sanda a jihar Kano sun kama wani Philibus Ibrahim kan zargin halaka budurwarsa yar shekara 22 mai suna Theresa Yakubu, jaridar The Punch ta rahoto.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ya rahoto cewa Ibrahim, wanda aka ce ya aikata laifin a karamar hukumar Tudun wada na jihar, an kama shi tare da abokin harkalarsa, Gabriel Bila, dukansu mazauna Unguwar Korau da ke Tudun Wada a yankin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kame tsagerun 'yan bindiga 2 da suka addabi jihohin Arewa

CP na Kano
Matashi a Kano ya yi ajalin budurwarsa yar shekara 22 a Kano. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mamman Dauda, ya tabbatar wa NAN hakan a ranar Talata a birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dauda ya ce:

"A ranar 2 ga watan Afrilu misali karfe 4.30 na yamma, mun samu rahoto daga wani dan kasa na gari cewa ya ga wata mace a kwance a gefen titi ba ta numfashi a hanyar Kano zuwa Jos a kauyen Anadaria.
"Bayan samun bayanin, tawagar yan sanda sun garzaya zuwa wurin kuma suka garzaya da wanda abin ya faru da ita zuwa Babban Asibitin Tiga inda likitoci suka tabbatar ta rasu.
"Bincike, amma, ya nuna cewa wacce abin ya faru da ita ta taro Nasarawan Kuki don zuwa kauyen Yantomo a karamar hukumar Babba na jihar Kano a ranar 27 ga watan Maris misalin karfe 6 na yamma.
"A yayin binciken, an kama tsayayyen wanda ake zargi ya aikata laifin kuma ya amsa hakan ta hanyar amfani da gyalen wacce abin ya same ta don shake ta."

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Matar Gwamnan Kano Na Farko, Ladi Bako, Ta Rasu Tana Da Shekaru 93

Dauda ya ce ana cigaba da zurfafa bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

An kama matasa 3 kan laifin sace wata yarinya a jihar Kano

A wani rahoton yan sanda na jihar Katsina sun yi nasarar kama wasu matasa uku kan zarginsu da sace wata yarinya yar shekara shida.

Gambo Isah, mai magana a yawun rundunar yan sandan Kano cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce matasan uku sun hada baki ne wurin sace yarinyar a unguwar Bachirawa a Kano a watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel