Matar Gwamnan Kano Na Farko, Ladi Audu Bako, Ta Kwanta Dama

Matar Gwamnan Kano Na Farko, Ladi Audu Bako, Ta Kwanta Dama

  • Hajiya Ladi Bako, matar gwamnan jihar Kano na farko, Audu Bako, ta kwanta dama tana da shekaru 93 a duniya
  • Dattijuwar matar ta rasu a yau Laraba, 5 ga watan Afrilu bayan ta yi fama da rashin lafiya wanda ya kai ga kwantar da ita a asibiti
  • Za a yi jana'izarta da misalin karfe 2:00 na rana a fadar sarkin Kano da ke Kofar Kudu

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa Allah ya yi wa matar gwamnan jihar Kano na farko, Hajiya Ladi Audu Bako rasuwa tana da shekaru 93.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa diyar marigayiyar, Zaina Bako ta tabbatar mata da labarin mutuwar mahaifiyar tasu a ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu.

Marigayiya Hajiya Ladi Audu Bako
Matar Gwamnan Kano Na Farko, Ladi Audu Bako, Ta Kwanta Dama Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Marigayiya Ladi ta yi fama da rashin lafiya har ta kwanta a asibiti

Kara karanta wannan

Rashin Tausayi: Matashi A Kano Ya Yi Ajalin Budurwarsa Yar Shekara 22 Mai Juna Biyu Ta Hanyar Shake Wa

An tattaro cewa tsohuwar ta rasu ne a asibitin kwararru na Prime da ke jihar Kano bayan ta yi fama da rashin lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a yi jana'izarta da misalin karfe 2:00 na rana a fadar sarkin Kano da ke Kofar Kudu kamar yadda diyarta ta bayyana, rahoton jaridar Leadership.

An nada mijinta a matsayin gwamnan jihar tsohuwar Kano a lokacin mulkin soja daga Mayun 1967 zuwa watan Yulin 1975.

Ya yi gyare-gyare da dama da kuma gina makarantu da dama a fadin jihar.

Kotun Kano ta yi umurnin yanka wani zakara ranar Juma'a saboda yana cara

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke zaune a Gidan Murtala a garin Kano ta zartar da hukunci a kan wata kara da wasu mutane suka shigar da makwabcinsu mai zakara.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Dan Basaraken Kano

Makwabtan mutumin mai suna Isyaku Shu'aibu sun yi kararsa a kotu bisa zargin cewa zakaransa na hana su walawa a unguwa saboda tsananin caransa kuma yana hana su baccin jin dadi.

Bayan sauraron karar, mai shari'a Halima Wali ta umurci mai zakaran da ya killace shi sannan kuma ya yanka shi saboda ya daina damun mutane.

A haka ne sai mai zakaran ya nemi alfarmar a ba shi zuwa ranar Juma'a kafin ya yanka shi inda kotu ta amsa bukatar tasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel