Kotun ƙoli tayi Fatali da Ƙarar Nwajiuba dake Fatan Ta Nuna Rashin Cancantar Takarar Tinubu da Atiku

Kotun ƙoli tayi Fatali da Ƙarar Nwajiuba dake Fatan Ta Nuna Rashin Cancantar Takarar Tinubu da Atiku

  • Tsohon ministan na ilimi, ya ce kotu ta soke takarar Tinubu saboda baisan
  • Nwajiuba yace a ina Tinubu ya samu N100, 000,000 na siyan fam ba
  • Ya kuma kalubalanci yadda aka bi aka fitar da Tinubu da Atiku Abubakar na APC da PDP takara

Abuja - Babbar kotu da kotun ɗaukaka ƙara duka sunyi fatali da ƙararrakin, inda suka ce shari'ar ta rasa dalili kwakkwara da za'a saurare ta, kuma lokaci ya wuce.

Babbar Kotun Koli ta ƙasa, ta kori ƙarar da tsohon ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya shigar.

Inda yake neman kotun data ayyana takarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bila Ahmed Tinubu na APC da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP sukai a matsayin haramtacciyar takara.

Nwajiuba
Kotun ƙoli tayi Fatali da Ƙarar Nwajiuba dake Fatan Ta Nuna Rashin Cancantar Takarar Tinubu da Atiku Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Sayen kuri'u: An kori wata karar da ministan Buhari ya shigar kan Tinubu da Atiku

Biyo bayan shigar da ƙarar da yayi, yanzu haka babbar kotun tayi fatali da ƙarar nan take ba tare da cigaba da wahalar da shari'a ba.

Da yake fatali da ƙarar, mai Shari'a Inyang Okoro, ƙarƙashin kwamitin mutane biyar, yace tsohon ministan bai shigar da ƙarar a kan lokacin da doka ta tana da ba.

Tunda fari dai, Nwajiuba da wata ƙungiya mai fafuta ta al'umma, sun kalubalanci Tinubu ne akan a ina ya samu N100, 000,000 daya sayi tikitin nuna sha'awar sa ta samun takara kamar yadda jaridar The punch ta sanar.

Wanda suka ce hakan ya saɓawa sashen doka na 90 (3) na dokar zaɓe ta 2022.

Minista Nwajiuba ya ƙara ɗaukaka ƙara zuwa kotun gaba, amma aka kore ta inda aka yanke hukuncin cewa, shari'ar ta zama lalatacciya saboda an ɓata lokaci akan ta kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ƴan Shi'a Sun Dirar wa Abuja, Suna Nema A Bawa El-Zakzaky Fasfo ɗin sa

Tun a baya, tsohon ministan ya roƙi kotun koli data soke hanyar da aka bi, aka zaɓi Atiku da Tinubu a matsayin masu takarar APC da PDP.

Itama Jaridar The Cable tace, Nwajiuba bai samu nasarar ko ɗaya ba yayin da yasha kashi a dukkan shari'ar guda biyu inda ake ce masa shari'ar ta rasa dalili kwakkwara da zai sa a saurare ta a gaban kotu.

Kotun Ɗaukaja Ƙara a Osun Zata Zartar da Hukuncin akan Zaɓen Gwamna.

A wani labari mai kama da wannan, kotu na ƙoƙarin sanar da sahihin gwamnan jihar Osun, kotun ɗaukaka ƙara zata yanke hukunci akan wanda yaaahe zaɓen jihar Osun. Kamar yadda Jaridar Legit ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel