“Miyanki Ko Dadi Babu”: Matashiya Ta Fadawa Surukarta Ido Cikin Ido Ba Tare Da Tsoron Komai Ba

“Miyanki Ko Dadi Babu”: Matashiya Ta Fadawa Surukarta Ido Cikin Ido Ba Tare Da Tsoron Komai Ba

  • Wani bidiyo da ya nuno wata matashiya tana kushe miyan uwar mijinta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Matar ta fada ma surukar tata cewa miyanta ya yi gishiri da yawa, tana mai mamakin dalilin da yasa take girki haka
  • Yayin da ake daukar bidiyon, furucin da surukar ta yi ya baiwa uwar mijin dariya yayin da masu amfani da TikTok suka jinjinawa alakarsu

Wata matashiya yar Najeriya @mumryan23 ta wallafa dan gajeren bidiyo da ke nuno lokacin da ta kushe miyan uwar mijinta.

Da take fuskantar matar, matashiyar ta fada mata cewa miyan da ta girka bai da dadi ko kadan. Matar ta cika da mamaki.

Matashiya tare da uwar mijinta
“Miyanki Ko Dadi Babu”: Matashiya Ta Fadawa Surukarta Ido Cikin Ido Ba Tare Da Tsoron Komai Ba Hoto: @mumryan23
Asali: TikTok

Matashiya da uwar mijinta

Ta roki matashiyar a kan ta yi hakuri da girkin haka saboda ta sa dan guntun nama da kifi a miyan. Duk da cewar matashiyar ta ce miyan ya yi kamar gishiri ya yi yawa a ciki, uwar mijin ta murmusa ne kawai.

Kara karanta wannan

"Zan Koma Gida": Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar ta yi mamaki kan yadda mijinta ya dungi cin abincinta. Mutane da dama da suka kalli bidiyonsu sun ja mamakin alakar da ke tsakanin matan biyu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@pretty mary kay ta ce:

"Ina kaunar matar nan."

@nanaaeesha085 ta ce:

"Idan uwar mijina ce tsine maki kawai za ta yi."

@Mycoranski ya ce:

"Kada ki gwada wannan da mahaifiyata."

@temitope Temmy Gold ta ce:

"Irin wannan uwar mijin sun yi karanci."

@Ajokeade ta ce:

"Zuciyar alkhairi uwar tagari."

@ oluwaseyi ta ce:

"Dan Allah mijinki bai da masoyiya matar nan na da kirki sosai."

@brokezz ya ce:

"Ki gwada wannan da mahaifiyata sannan ki tsinci kanki a babban asibiti."

@Odunayo_me ya ce:

"Wannan surukar taki tana da sanyi faaaa."

@user1029695316808 ya ce:

"Uwar miji tamkar uwa kawai dariya take yi Allah ya yi mata albarka."

Kara karanta wannan

Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Yi Kuka Da Hawaye Saboda Rashin Saurayi, Bidiyon Ya Yadu

Matata shekarunta 21 ba 11 ba, magidanci ya yi karin haske

A wani labari, wani mutumi da shekarunsa suka dan ja ya yi karin haske kan rade-radin da wasu ke yi cewa ya auri karamar yarinya yar shekaru 11 duk da shekarunsa.

Mutumin ya ce sam matarsa shekarunta 21 kuma auren soyayya suka yi don duk sukna kaunar junansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel