“Shekarun Matata 21”: Dan Najeriya Da Aka Zarga Da Auren Karamar Yarinya Ya Yi Karin Haske

“Shekarun Matata 21”: Dan Najeriya Da Aka Zarga Da Auren Karamar Yarinya Ya Yi Karin Haske

  • Wani dan Najeriya da aka zarga da auren karamar yarinya ya yi martani a soshiyal midiya don ya wanke kansa daga zargin
  • Mutumin wanda ya fito daga arewacin Najeriya ya ce shekarun matarsa 21 sabanin rade-radin da makirai ke yi cewa shekarunta 11
  • Angon ya bayyana cewa auren soyayya suka yi da amaryarsa babu wanda ya yi mata aure bisa dole

Wani mutumi da ya bayyana sunansa Aminu Danmaliki a Facebook ya yi karin haske kan zargin da ake masa cewa ya auri karamar yarinya da bata balaga ba.

Mutumin dan arewa ya ce matarsa ta dara shekaru 21 kuma shi bai auri yarinya yar shekaru 11 ba kamar yadda ake zarginsa.

Aminu Danmaliki ya ce shekarun matarsa ba 11 ba
“Shekarun Matata 21”: Dan Najeriya Da Aka Zarga Da Auren Karamar Yarinya Ya Yi Karin Haske Hoto: @aminudanmaliki
Asali: Facebook

Da yake nanata cewar duk zargin da ake masa karya ne, ya bayyana cewa da yardar matar aka yi auren kuma su dukka suna son junansu.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Sace Yar Shekara 5 Da Matasa Biyu a Jihar Kwara

Karanta cikakkiyar sanarwar da ya yi a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Aurena na baya-bayan nan da Sakina ya haddasa tashin hankali sosai da kuma zargi mara tushe cewa na auri karamar yarinya da bata balaga ba wasu sun ce shekarunta 11 kuma cewa dole aka yi mata ta aure ni. Wannan ba gaskiya bane. Bidiyon auren ya yadu. Mun yanke shawarar yin shiru amma aka shawarce ni da na fito na fadi zahirin gaskiya, ga shi nan: Shekarun matata abun kaunata 21 ita ta zabe ni a matsayin mijinta kuma nima ina sonta. Ina fatan masu bita da kulli da masu shakku za su ga zahirin gaskiya a hoton nan sannan su barmu mu ci amarcinmu."

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka yi martani ga jawabin nasa sun kuma taya mutumin murnar aurensa sannan suka yi masa fatan samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Adamawa 2023: A Karshe Gwamna Fintirtiri Ya Magantu Kan Ayyana Zaben a Matsayin Wanda Bai Kammalu ba

Ga wallafar tasa a kasa:

Martanin jama'a

Abubakar Ibrahim Gabari ya yi marta:

"@Aminu Danmaliki Ranka ya dade Allah ya Baku zaman lpy ,tunda abin da kayi ya halatta a Shari a Kuma koyi ne ga fiyayyen halitta annabi muhammad S.A.W."

Usman Samba ya ce:

"Honey Moon dai Alaji. Azumi fa zaa fara Lol.
"Allah ya bada zaman Lapiya madauwami na har Abada."

Hon Abubakar A Sodangi ya ce:

"Allah yasanya albarka chikin wannan aure Allah yabada zuri'a dayyiba ."

Muhammad Ath-thaaniy Yunusa Al-kanawiy ya ce:

"Duk abin da suka yi, ku kuka ja, ya kamata mutum ya sirrinta iyalinsa, amma an saki clips haka, dole ne a biya farashin yan soshal midiya."

A baya mun kawo cewa jama'a sun yi ta cece kuce bayan cin karo da bidiyon auren magidancin da tsaleliyar amaryarsa saboda ganin tana da kuruciya sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng