“Na Rasa Mashinshini”: Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Yi Kukan Rashin Saurayi a Bidiyo

“Na Rasa Mashinshini”: Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Yi Kukan Rashin Saurayi a Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya don kokawa kan kalubalen da take fuskanta
  • A cewar dalibar, ba za ta iya bugan kirji ta ce tana da saurayi ba a shekarunta kuma bata da mai daukar dawainiyarta
  • Matashiyar mai shekaru 20 ta zubar da hawaye yayin da take rokon Allah ya kawo mata dauki, tana mai cewar za ta yi wa tufkar hanci

Wata matashiyar budurwa yar shekaru 20 ta bayyana a soshiyal midiya cewa bata da saurayi kuma hakan bai mata dadi ba.

Budurwar mai suna Princess ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya yadu a TikTok inda ta zubar da hawaye.

Budurwa a cikin yanayi na damuwa
“Na Rasa Mashinshini”: Budurwa Yar Shekaru 20 Ta Yi Kukan Rashin Saurayi a Bidiyo Hoto: @officia_princess
Asali: TikTok

Princess ta bayyana cewa har yanzu ita daliba ce, bata da mai daukar nauyinta kuma 'hayaki' kawai take da shi a matsayin aboki. Da take ci gaba da bayani, ta ce zata kawo karshen abubuwa nan ba da jimawa ba tana mai rokon Allah ya kawo mata dauki.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Uba Ya Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Diyarsa Ta Zo Ya Sanya Mata Albarka a Wajen Bikin Aurenta

Bidiyon nata ya yi fice a dandalin yayin da mutane da dama suna karfafa mata gwiwa, suna masu lallashinta da kada ta yi abu mara kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ba a sani ba ko kawai neman suna take yi da bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Djpetrotee the blessed ta ce:

"Ki ci gaba da karatu akwai lokacin duk wadannan abubuwan kawai dai ki mayar da hankali inda kika sanya gaba."

kimaniivassel ta ce:

"Kina da matukar kyau me yasa kike da wannan a zuciyarki."

Ricardo Hibbert245 ya ce:

"Ke bakar mace yar Afrika ce mai karfi kada ki bari komai ya dame ki kin ji."

Florence ta ce:

"Zan iya zama aminiyarki idan ba za ki damu ba don na fada maki komai na tarihin rayuwata."

JoshFlamez ta ce:

"Ki kwantar da hankalinki yarinya idan da rai da rabo."

Kara karanta wannan

“Zan Fasa Auren”: Kyakkyawa Amarya Ta Ajiye Kunya Ta Tika Rawa Iya Son Ranta a Wajen Bikinta, Bidiyon Ya Yadu

Young Star ya ce:

"Yi hakuri yar'uwa na fahimci yadda kike ji gani nan zan kasance tare da ke a yanzu."

Mijina ya rabu dani saboda ina cin amanarsa da wasu maza biyu - Matashiya ta koka

A wani labari na daban, wata matashiyar mata ta bayyana yadda aurenta ya hadu da tangarda bayan mijinta ya gano tana da wasu samari biyu bayan shi.

A cewarta mijin ya san tana cin amanarsa amma sam bai san cewa mazan sun kai mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel