Ba'a Kai Hari Gidan Shugaban Hukumar Zabe INEC Ba, Oyekanmi

Ba'a Kai Hari Gidan Shugaban Hukumar Zabe INEC Ba, Oyekanmi

  • Shugaban hukumar INEC ta kasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya musanta labarin da ake jingina masa na kai hari gidansa a Bauchi
  • Rotimi Lawrence Oyekanmi, sakataren watsa labarai na Ciyaman din INEC, ya ce Bidiyon da ake yaɗa wa bau da alaƙa da uban gidansa
  • Wasu bayanai sun nuna cewa bidiyon harin da aka kai gidan Rarara ne yanzu aka jingina wa shugaban INEC da sunan gidansa ne a Bauchi

Abuja - Shugaban hukumar zaɓe ta kasa mai zamaɓ kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya musanta rahoton cewa an kai hari gidansa da ke jihar Bauchi, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Babban sakataren watsa labarai na Ofishin shugaban INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

Mahmud Yakubu.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya ce Farfesa Mahmud Yakubu, bai mallaki kadarar gidan da ake zance ba, a jihar Bauchi ko kuma wani wuri daban a faɗin duniya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Bayanai sun nuna cewa bidiyon da ke yawo na harin da wasu matasa suka kai gidan shahararren mawakin siyasan nan, Dauda Rarara, shi ne aka jingina wa shugaban INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin dagaske an kai wa gidan Yakubu Hari?

A sanarwan, Mista Iyekanmi ya ce:

"Kadarar gidan da aka rahoto wasu fusatattun matasa sun kaiwa hari a wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ba ta da alaƙa kuma ba mallakin shugaban hukumarINEC ba ne."
"Wannan shi ne baya-bayan nan a jerin kamfen da wasu bara gurbi suka kudiri aniya don karkatar da hankulan mutane. Muna kira ga ɗaukacin yan Najeriya su yi fatali da bidiyon."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa shugaban INEC, Mahnud Yakubu, na shan suka musamman daga ɓangaren yna adawa, waɗanda suka yi rashin nasara a zaben shugaban kasa.

Tsohon shugaban sojin Najeriya ya mutu

A wani labarin kuma Tsohon shugaɓan rundunar soji kuma mutum na biyu a mulkin Marigayi Abacha, Oladipo Diya, ya kwanta dama.

Shi ne mutum na biyu mai karfin faɗa a ji a mulkin Abacha wanda a yanzu zamu iya kiransa da mataimakin shugaban kasa.

Gwamnatin Abacha ta kama shi da zargin hannu a yunkurin cin amanar ƙasa a 1997 amma ya kubuta bayan mutuwar Abach a 1998.

Asali: Legit.ng

Online view pixel