Zan Fi Baiwa Fannin Biyan Albashin Ma’aikata Fifiko a Mulkina, Inji Sabon Gwamnan Jihar Abia

Zan Fi Baiwa Fannin Biyan Albashin Ma’aikata Fifiko a Mulkina, Inji Sabon Gwamnan Jihar Abia

  • Sabon gwamnan Abia ya bayyana kadan daga abubuwan da ya tsara yi idan aka rantsar dashi a watan Mayu
  • Ya ce zai yi aiki da tawagar kwararru don tabbatar da komai ya tafi yadda ake bukata a fannin tattalin arziki
  • Hakazalika, ya ce zai ba fannin biyan albashin ma’aikata fifiko a mulkinsa don jin dadin ma’aikata a jihar

Jihar Abia - Zababben gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya bayyana cewa, biyan albashin ma’aikata shine zai zama babban abin da zai fi mayar da hankali a kansa idan aka rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu.

Otti ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Arise Tv da safiyar ranar Alhamis 23 ga watan Maris.

Ya kara da cewa, ya kamata ‘yan jihar su kwana da sanin cewa, za su ga sauyi na tsaruka da yawa a jihar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

Alex Otti ya yi alkawarin mai da hankali kan albashin ma'aikata
Alex Otti, zababben gwamnan jihar Abia da ke Kudu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Otti ya banke dan takarar PDP a zaben gwamna

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Otti na jam’iyyar Labour ne ya lashe zaben gwamna a jihar Abia, inda ya samu kuri’u 175,467.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya banke abokin hamayyarsa da ya zo na biyu dan jam’iyyar PDP, Okey Ahiwe mai kuri’u 88,529 a zaben na bana.

Jam’iyyar Labour ta fi karbuwa a yankin Kudu maso Gabas, yankin da dan takarar shugaban kasanta, Peter Obi ya fito.

Abubuwan da Otti ya tsara

A cewarsa lokacin da yake jawabi:

“Ya zuwa jiya, na fara magana da bankuna. Abin da za su tsammanta shine kawai gyara ta ko ina a jihar Abia.
“Babu laifi a cin bashi, amma matsalar ita ce abin da za ku yi da kudin da aka ci. Biyan albashi ne babban abin da zan sa a gaba.

Kara karanta wannan

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

“Za mu kirkiri tattalin arziki mai girma, mu habaka tattalin arziki, za mu yi duk mai yiwuwa don ganin tattalin arzikinmu ya girma.”

Yadda zai kawo masu taimaka masa

Ya kuma shaida cewa, zai nada wata tawagar da za ta taimaka masa a tafiyar da gwamnatinsa nan ba da jimawa ba.

A kalamansa:

“Nan da kwanaki masu zuwa, zan nada wata tawagar da za a rantsar da ita a ranar 29 ga watan Maris. Zan nada mutanen da suka cancanta domin su taimake ni.
“Za mu duba abubuwa masu yawa, amma za mu yi hakan mataki-mataki, ciki har da kudaden shiga.”

Jihar Abia na daya daga cikin jihohin da aka samu tsaiko har aka dage tattara sakamakon zaben gwamna, daga baya aka gama tattara komai ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel