Babban Bankin Najeriya (CBN) Zai Sako Tsofaffin Takardun Kudi

Babban Bankin Najeriya (CBN) Zai Sako Tsofaffin Takardun Kudi

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayar da kai bori ya hau, zai sako tsofaffin takardun kuɗi ga ƴan Najeriya
  • Babban bankin ya kuma umurci bankuna da su fara ba mutane tsofaffin kuɗin domin su wadace su
  • Wannan matakin ba ƙaramin sauƙaƙa raɗaɗin da ƴan Najeriya suke ciki zai yi ba a dalilin sauya fasalin takardun kuɗi

Abuja- Babban bankin Najeriya (CBN) ya kammala shirye-shirye tsaf domin sako dukkanin tsofaffin takardun kuɗi na N1,000, N500 da N200 a hannun shi zuwa ga bankuna. Rahoton Punch

Wannan matakin ana sa ran zai kawo ƙarshen watannin da ƴan Najeriya suka kwashe suna shan wahala akan sauya fasalin kuɗi da babban bankin Najeriya (CBN) yayi.

Emefiele
Babban Bankin Najeriya (CBN) Zai Sako Tsofaffin Takardun Kudi Hoto: Tribune
Asali: Getty Images

Wannan sabon matakin na babban bankin na zuwa ne bayan an kwashe makonni da dama tun umurnin da kotun ƙoli ta bayar na tsofaffin takardun kuɗin su cigaba da zama halastattu har sai zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Canjin Kuɗi: Gwamnan CBN Ya Baiwa Yan Najeriya Hakuri, Ya Aike Musu da Sako Mai Muhimmanci

A ranar Laraba da daddare, manyan jami'an bankin CBN da na wasu bankunan, sun tabbatar da cewa gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ya bayar da umurnin cewa bankuna su fara rabawa mutane tsofaffin kuɗin daga yau (Alhamis)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa, CBN zai fara ba bankuna tsofaffin takardun kuɗin daga ranar Alhamis. Rahoton The Nation

Godwin Emefiele ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci a ranar Laraba da yamma, inda ya gaya musu cewa babban bankin zai fara basu tsofaffin kuɗin da yake da su daga ranar Alhamis.

Majiyoyi masu ƙarfi a wajen taron sun bayyana cewa CBN zai kuma soke kayyade damar cire kuɗi da ya sanya wacce ta kwashe lokaci mai yawa.

Haka kuma, bankin CBN ya bayyana cewa daga yanzu idan kwastomomi za su kai tsofaffin kuɗin su basu buƙatar sai sun samo lambobi kamar yadda ake yi a baya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rikici Ya Kara Tsananta a Kano, An Wargaza Akwatunan Zabe Sama da 10

Dangote Ya Samu Naira Biliyan 460 a Cikin Kwana 1, Ya Zama Attajiri na 83 a Duniya

A wani labarin na daban kuma, arziƙin Dangote ya ƙara hauhawa cikin kwana ɗaya, ya ƙara matsawa sama a cikin jerin attajiran duniya.

Hamshakin attajirin ya samu naira biliyan 460 a cikin kwana ɗaya tal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel