Sauya Fasalin Naira: Gwamnan CBN Ya Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Abu 1

Sauya Fasalin Naira: Gwamnan CBN Ya Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Abu 1

  • Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya baiwa 'yan Najeriya hakuri bisa matsalolin da suka fuskanta wajen hada-hadar kuɗi ta Intanet
  • Emefiele ya ce sun gamu da wasu kalubale ne amma yanzun an warware duk wata matsala da ta kawo cikas
  • Ya gargaɗi masu bankuna da suka kwana da shirin cewa idan suka aikata ba daidai ba zasu rasa lasisinsu

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya baiwa 'yan Najeriya hakuri kan matsalolin da suka fuskanta yayin tura kuɗi ta asusun banki da sauran hada-hadar Intanet.

The Nation ta tattaro cewa gwamna Emefiele ya nemi afuwar 'yan Najeriya yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron kwamitin MPC ranar Talata.

Gwamnan CBN.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele Hoto: CBN
Asali: Getty Images

Gwamnan CBN ɗin ya amince cewa, "mun gamu da wasu Kesa-Kesai da suka nemi su sha karfinmu," amma a halin yanzun an warware babu sauran wata matsala.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam El-Rufai Ta Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Siyasa Dake Shirin Ta Da Yamutsi

Da yake amsa tambayoyi kan ko suna jin kamshin wasu bankuna a Najeriya za su rushe duba da ƙaruwar rushewar bankuna a Amurka, Emefiele ya ce bankunan Najeriya ba su shiga haɗari ba sanadin abinda ke faruwa a Amurka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya tabbatar da cewa bankunan Najeriya na cikin tsaro kuma hakan ya samo asali ne daga dokoki da ƙa'idojin da CBN ya gindaya don kare bankuna daga ibtila'in rushewa wanda zai sa mutane su rasa kuɗin da suka aje.

Punch ta rahoto a kalaman Emefiele ya ce:

"Babu kwastoman da ya rasa kuɗin da ya aje sakamakon matsalar bankuna tun 2008 saboda ƙa'idojin da muka gindaya don karewa mutane kuɗadensu."

Bugu da ƙari, gwamnan CBN ya gargaɗi masu hannun jari a bankuna da su kwana da sanin cewa, "Lasisin kafa banki alfarma ce ba dama ba, zamu iya soke shi idan suka yi rashin ɗa'a."

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Naɗa Sabbin Hadimai 30 Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki

"Mun gwammace mu raba gari da masu hannun jari da mu jefa kuɗaɗen yan Najeriya cikin haɗari."

Wani mazaunin cikin garin Kaduna, Musa Abubakar, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa yana gab da yin Allah ya isa game da kuɗinsa da suka maƙale.

Ya ce sama da mako biyu ya tura kuɗi ta asusun bankinsa, sun fita amma har yanzun ba su shiga asusun wanda ya tura mawa ba.

"Muna fatan su warware matsalar tunda suna sane, muna fama da tasgaro a hada-hadar kuɗi ta Intanet, wani lokacin ka tura su ƙi tafiya, wani lokacin kuma ba zasu je a kan lokaci ba."

Haka nan wani mai sana'ar siyar da kayan abinci, Isma'il Idris, ya ce gaskiya an shiga matsala babba, babu Kash kuma tura kuɗin ma ba bu tabbas din ya yi.

"Muna fatan CBN ya gaggauta kawo karshen matsalar cikin sauri amma ba neman afuwa mu ke buƙata ba," inji shi.

Kara karanta wannan

Batun Hango Ranar Mutuwar Sa, Shahararren Fasto Ya Fito Ya Bayyana Gaskiyar Zance

Gwamna Adeleke ya gargaɗi bankunan Osun

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Osun ya fusata, ya umarci bankuna su daina baiwa talakawansa tsoffin kuɗin da aka canja

Ademola Adeleke, ya ce ba zai yuwu yana ji yana gani bankuna su zalunci mutanen jiharsa ba kuma ya kama bakinsa ya yi shiru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel