Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Abba Kyari Kan Rushe Tuhumarsa da Ke da Harkallar Kwaya

Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Abba Kyari Kan Rushe Tuhumarsa da Ke da Harkallar Kwaya

  • Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya yi watsi da bukatar Abba Kyari na neman soke tuhumarsa da ake da harkallar kwaya
  • Kyari da abokansa da ke gaban kotu sun nemi a tattara tuhume-tuhumen da ake musu tare da watsar dasu, kamar yadda lauyoyinsu suka gabatar
  • Sun bukaci kotun da ta dakata da shari’arsu, inda suka ce ba a ladabtarsu a cikin gida ba daidai da ka’idar rundunar ‘yan sanda

FCT, Abuja Babban kotun tarayya a Abuja ya yi watsi da bukatar Abba Kyari da abokan harkallarsa kan bukatar soke zarge-zargen da ke kansu game da harka da miyagun kwayoyi.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar Laraba 22 ga watan Maris a gaban kotun, inda Kyari ya ce ya kamata a dakata da batun tuhumarsa kan kwaya tukuna, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan ta'adda sun kone wani babban kotu a wata jiha, sun barnata kayan aiki

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Emeka Nwite ya yi watsi da bukatar, inda yace kotun na da dama da ikon sauraran batutuwa da suka shafi harkallar kwaya, kamar yadda yazo a kundin dokar NDLEA.

Abba Kyari ya roki a duba lamarinsa
Abba Kyari, tsohon dan sandan da ake zargi da hannu a harkallar kwaya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Bukatar Kyari a gaban kotu

Channels Tv ta ruwaito cewa, alkalin ya kuma kara da cewa, sashe na 251 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kotun ikon sauraran irin wannan kara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kyari ya shaidawa kotun cewa, shigo da batun gaban kotu ya yi wuri, inda yace NDLEA ta yi gaggawa a madadin ta bari a bincike shi a cikin gida; a hukumar ‘yan sanda.

Haka kuma ya shaidawa kotun cewa, tuni hukumar ‘yan sanda ta fara bincike game da lamarin kuma ta fara fitar da rahoto game da hakan.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohuwa ta rude, ta kone danta, matarsa da jikokinta a wata jiha

A fahimtarsa, ya kamata a titsiye shi a gaban kotu ne bayan kammala binciken hukumar ‘yan sanda sabanin yadda aka yi a yanzu.

Kitimurmurar Kyari da NDLEA

Kyari, wanda tsohon jami’in dan sanda ne a runduna ta musamman ta IRT na fuskantar tuhumar NDLEA da hannu a harkallar miyagun kwayoyi.

An maka Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda hudu na IRT; ACP Sunday J. Ubua, ASP Bawa James, Sufeta Simon Agirgba da Sufeta John Nuhu a gaban babban kotun tarayya.

An ruwaito cewa, ana zarginsu da shigo da kayan maye na hodar iblis da yawansa ya kai kilo-giran 17.55.

A baya, wani ya yi bayanin yadda Abba Kyari ya yi masa alkawarin kudade masu yawa idan ya yiwa Bukola Saraki sharri.

Asali: Legit.ng

Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel