Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

  • Ayoade Akinnibosun yana ikirarin DCP Abba Kyari yi masa alkawarin kudi da bizar zuwa kasar waje
  • Wannan mutumi da ake tuhuma da laifin fashi da makami ya ce an bukaci yayi wa Bukola Saraki kazafi
  • Da farko Akinnibosun ya turje, amma da barazana tayi yau sai ya aikata abin da ake bukata a wajensa

Kwara - Daya daga cikin wadanda ake tuhuma da laifin yin fashi da makami a garin Offa da ke jihar Kwara, Ayoade Akinnibosun ya bayyana a kotu.

Ayoade Akinnibosun ya je gaban babban kotun jihar Kwara da ke zama a garin Ilorin, Punch ta ce a nan ne ya jefa DCP Abba Kyari a katuwar matsala.

Mista Akinnibosun ya fadawa Alkalin kotun cewa tsohon shugaban dakarun IRT, Abba Kyari ya azabtar da shi, sannan ya yi masa alkawarin miliyoyi.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Da Shagalin Biki An Fasawa Amarya Ido a Jihar Kano, yace ba zai yarda ba

Wanda ake zargi da laifin fashin yake cewa DCP Kyari wanda yanzu yana tsare, ya ce zai ba shi N10m idan har ya iya lakawa Dr. Bukola Saraki sharri.

Ga alkawarin kudi ga bizar ketare

An rahoto wanda ake tuhuma ya ce baya ga batun kudi, ‘dan sandan ya ce zai ba shi bizar zuwa duk kasar da yake sha’awa idan ya biya masa bukatarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wannan mutumi, bai karbi tayin da aka yi masa na yi wa tsohon shugaban majalisar sharri ba, hakan ya sa ya sha wahala a hannun ‘yan sanda.

Bukola Saraki
Tsohon Gwamna, Bukola Saraki a Ilorin Hoto: @bukolasaraki
Asali: Twitter

Kamar yadda Tribune ta rahoto shi yana fada a kotu, Akinnibosun ya ce a gabansa aka azabtar da wasu, aka harbe su saboda su jefa Saraki a matsala.

Ba zan yi wa mutum sharri ba

Shi (Kyari), ya ce in amsa cewa Saraki ne ya fada mana mu je yi fashi. Na fada masa ba zan iya yin haka ba, sai dai in mutu da in yi wa mutum sharri.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Kama Jarumin da ya Caka wa Makwabcinsa Wuka a Kirji kan N1,000

Sai ya fada mani in yi tunani da kyau, daga nan ya umarci ‘yan sanda biyu; Hassan da Mashood su maida ni wani daki, dabam da inda mutane suke.

- Ayoade Akinnibosun

A gaban Akinnibosun jami’an ‘yan sanda suka kashe mutane biyar, da aka kashe wani abokin aikinsa a gabansa, dole ya yarda ya lakawa Saraki sharri.

Mutane biyar ake zargi da laifin fashi a Offa, su ne; Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salaudeen Azeez da wani Niyi Ogundiran.

Ku zabi mijina - Remi Tinubu

Rahoto ya zo cewa Oluremi Tinubu ta nemi alfarma wajen ‘Yan Najeriya su zabi Mai gidanta mai neman mulkin kasar nan a inuwar APC a zaben da za ayi.

Sanata Tinubu, Hajia Nana Shettima, Dr Falmata Zulum, Betta Edu, Hajia Nana Shettima da Barr. Chioma Uzodimma sun halarci kamfe na mata a Imo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel