'Yan Bindiga Sun Rike Wani Mutumin da Ya Kai N2m Na Fansar Matarsa Da ’Ya’yansa 3 da Aka Sace

'Yan Bindiga Sun Rike Wani Mutumin da Ya Kai N2m Na Fansar Matarsa Da ’Ya’yansa 3 da Aka Sace

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kaduna ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka rike wani mutumin da ya kai musu kudin fansa
  • Wannan lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan kashe wata mata a yankin Janjala da ke karamar hukumar Kagarko
  • Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman a cikin shekarun baya-bayan nan

Jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun rike wani mutumin da ya kawo kudin fansa don a sake matarsa, dansa da ‘ya’yansa mata biyu da aka sace a Anguwar Janruwa da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

An ruwaito cewa, makwanni biyu da suka gabata ‘yan bindiga sun farmaki Anguwar Janruwa a yankin Janjala, inda suka sace matar aure Hauwa Abubakar, danta Idris Abubakar da ‘ya’yanta mata Ummi da Sadiya.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Masu sayen kuri'u sun taru, sun lakadawa jami'an EFCC duka a jihar a Arewa

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, wani dangin wadanda aka sacen, Audu Bajeko ya ce, dan uwan nasa, Abubakar Ardo ya kwashi kudi N2m domin kai wa ‘yan bindiga a inda suke a ranar Lahadi, amma suka rike shi.

'Yan bindigan Kaduna sun rike wanda ya kawo kudin fansa
Yadda 'yan bindiga ke barna a Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Miliyan 20 ‘yan bindigan ke nema

Ya bayyana cewa, bayan rike mutumin, sun nemi a biya kudin fansa N20m kafin su sako shi da dukkan iyalansa, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Da kusan karfe 5:30 na yamma ranar Lahadi, lokacin ne shugaban ‘yan bindigan ya kira don sanar dasu cewa sun rike mutumin da ya kawo N2M na fansa don a sake matarsa da ‘ya’yansa.
“Da aka tambaye shi meye yasa, dan bindigan ya ce adadin kudin da ya nema ba su mutumin ya kawo ba.”

Bajeko ya bayyana cewa, shugaban ‘yan bindigan ya ce ba zai saki dukkan ahalin ba har sai an cika N18m na fansan su.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Wurin Raba Kayayyakin Zabe, Sun Tafka Barna

Ya kara da cewa, a halin da ake ciki kowa a dangin ya shiga tashin hankali, inda yace N2m din ma da aka hada an sha fama matuka ainun.

Akwai matsalar ‘yan bindiga a Janjala, shugaban yanki ya koka

Madakin Janajal, Samaila Babangida, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, lamarin ‘yan bindiga na ci gaba da jefa al’umma cikin mummunan hadari da rudani.

A kalamansa:

“Kwana biyun da suka gabata, aka kashe uwar gidan Ardo Fulani bayan karban kudin fansa N2m daga ahalin, da safen nan kuma muka samu labarin mutumin da ya je karbo iyalansa shi ma an rike shi bayan ba da N2m.”

Ya yi kira ga jami’an tsaro da su taimakawa al’ummar yankin ta hanyar taimaka musu da daukin yakar ‘yan bindigan da ke ta’addanci a yankin.

Ya zuwa yanzu, babu wani bayani daga hukumomin tsaro na ‘yan sanda soji har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

A jihar Borno kuma, sojoji sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP da suka kai hari cibiyar tattara sakamakon zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.