Shugaban Jam’iyyar PDP Na Jihar Ebonyi Ya Goyi Bayan Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC

Shugaban Jam’iyyar PDP Na Jihar Ebonyi Ya Goyi Bayan Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC

  • Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar
  • Ana ‘yar tsama tsakanin shugaban PDP da dan takarar jam’iyyar a jihar ta Ebonyi, lamarin da ya kawo rabuwar kai
  • Jam’iyyar Labour a jihar Ogun ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamnan PDP gabanin zaben gwamnoni

Jihar Ebonyi - Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi, Tochukwu Okorafor ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan APC a jihar, Francis Nwifuru.

Ya bayyana wannan goyon baya ga dan takarar APC ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a birnin Abakaliki na jihar ta Ebonyi, The Nation ta ruwaito.

Shugaban, wanda aka ce bai jituwa da dan takarar gwamnan PDP, Ifeanyi Odili ya bukaci jama’ar jihar da su ba da kuri’unsu ga dan takarar APC.

Kara karanta wannan

Taron dangi: Jam'iyyar Labour da PDP sun hade da nufin tsige gwamnan APC gobe Asabar

Yadda shugaban PDP a Ebonyi ya goyi bayan dan takarar APC
Jihar Ebonyi, a Kudancin Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kuma shaida cewa, yin adalci shine yankin Ebonyi North ta su dan takarar gwamnan APC ya samar da kujerar gwamna a bana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yi adalci, a ba kowa ya yi mulki

Ya yi bayanin cewa, ya kamata a yi adalcin ba kowanne yankin jihar damar yin mulkin karba-karba a duk sadda zabe ya taso, rahoton Naija News ta ruwaito.

A bangare guda, shugaban na PDP ya ce, dan takarar da jam’iyyar tasu ta fitar ba mutum ne mai gaskiya ba, kasancewar yana fuskantar tuhume-tuhume da yawa a gaban kotuna daban-daban na kasar nan.

A sanarwar da ya fitar, ya bayyana kotunan da dan takarar gwamnan na PDP ke amsa tuhume-tuhume, inda yace hakan zai iya shafar siyasa da kuma nagartar yiwa jihar aiki.

Yanzu dai saura sa’o’i kadan a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a Najeriya, kuma ‘yan siyasa na ci gaba da bayyana wadanda suke goyon baya.

Kara karanta wannan

Zaben Ranar Asabar: Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus Daga Awanni Kadan Kafin Zabe, Ya Bayyana Dalili

Jam’iyyar Labour ta hada kao da PDP don lallasa gwamnan APC Abiodun

A wani labarin kuma, dan takarar gwamnan PDP ya samu karuwa yayin da jam’iyyar Labour tace tana goyon bayansa a zaben gobe Asabar 18 ga watan Maris.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan kafin yin zaben da aka tsara yi na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a fadin kasar nan.

Jam’iyyar ta Labour ta ce, hadin kan jam’iyyun biyu ya zo ne duba da akidun siyasa da manufofi iri daya da suke dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel