Mutane 17 Sun Mutu, 17 Sun Jikkata a Wasu Hadurran da Suka Faru a Jihar Bauchi

Mutane 17 Sun Mutu, 17 Sun Jikkata a Wasu Hadurran da Suka Faru a Jihar Bauchi

  • Hukumomi sun bayyana yadda hadarin mota ya hallaka mutane da yawa a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas a Najeriya
  • Wannan lamarin ya faru ne a ranar Litinin 13 ga watan Maris, inda aka ce akalla mutum 17 ne suka kwanta dama
  • Rahoton da muka samo ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma irin raunukan da wasu suka samu a lokacin hadarin

Jihar Bauchi - Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 suka samu munanan raunuka a wasu hadduran da suka auku guda biyu a jihar Bauchi a ranar 13 ga watan Maris.

An ruwaito cewa, a hadarin farko, mutum 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da a na biyun kuma mutum shida suka kwanta dama.

A cewar tawagar hukumar kiyaye haddura da ke sintiri a yankin Azare zuwa Gamawa a jihar, daya daga cikin hadurran ya faru ne a kauyen Manaba da ke hanyar Zaki zuwa Gamawa, wanda ya rutsa da mutum 25.

Kara karanta wannan

Gobara Ta Tashi a Wani Banki a Kano, Ta Lakume Na'urorin ATM Guda 3

Yadda hadari ya kashe jama'a a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi a Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda haduran suka auku

Mutum 11 ne suka mutu nan take, ciki har da maza biyu da mata tara yayin da 13 suka tsira da raunuka; maza uku da mata 10, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadarin ya faru ne da wata motar kasuwa ta kamfanin Himma Express da wani Haruna Yusuf ke tukawa mai lambar KTG 13XF.

A hadari na biyun, an ce mutum shida ne suka kwanta dama nan take, inda wasu hudu kuma suka samu munanan raunuka.

A cewar rahoton hukumar FRSC daga ofishin Shira a karamar hukumar Shira dauke da sa hannun DRC TB Lawal, STO na ofishin Shira, hadarin ya faru ne a ranar Litinin 13 ga watan Maris, 2023.

Rahoton ya ce, hadarin ya faru ne a hanyar Yana zuwa Giade da nisan kilo mita 10 daga garin Yana, hedkwatar karamar hukumar Shira.

Kara karanta wannan

NSCDC Ta Kama Gangunan Man Fetur 150 Na Sata Za A Kai Su Kamaru Daga Akwa Ibom A Kwale-Kwale

An ce hadarin ya rutsa ne da wasu motoci biyu na kasuwanci; Golf 2 da Sharon mai lambar SHR 203 AA, daya motar kuwa babu lamba.

Ana gudun wuce iyaka

A cewar hukumar kiyaye hadurra, wannan hadarin ba zai rasa nasaba da gudun wuce iyaka da motocin ke yi ba, Punch ta ruwaito.

Hakazalika, hukumar ta ce maza hudu da mata biyu ne suka rasu a hadarin, yayin da maza hudu suka tsira da munanan raunuka.

Gobara da hadarin mota sun zama ruwan dare a Najeriya, a makon jiya ne wata kasuwa ta kama da wuta a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel