NSCDC Ta Kama Gangunan Man Fetur 150 Na Sata Za A Kai Su Kamaru Daga Akwa Ibom A Kwale-Kwale

NSCDC Ta Kama Gangunan Man Fetur 150 Na Sata Za A Kai Su Kamaru Daga Akwa Ibom A Kwale-Kwale

  • Jami'an hukumar tsaro na NSCDC a jihar Akwa Ibom sun yi nasarar kama gangunan man fetur a cikin kwale-kwale
  • An kama wasu mutane ne dauke da man fetur din a kalla ganguna 150 a cikin teku suna hanyar shigar da su Kamaru da barauniyar hanya
  • An kuma kama injinin zuko ruwa da suka yi amfani da shi wurin satar man fetur din daga bututu, za a gurfanar da su a kotu bayan bincike

Akwa Ibom - Hukumar tsaro ta NSCDC ta ce ta kama gangunan man fetur guda 150 da aka shigo su da barauniyar hanya a Akwa Ibom, The Cable ta rahoto.

Da ya ke magana yayin taron manema labarai a ranar Asabar, Yusuf Imam, kwamanda na NSCDC a jihar, ya ce jami'an hukumar sun kama mutum biyu da ake zargi a ranar Alhamis kuma sun kwace injin zuko fetur da aka yi amfani da shi wurin satan man.

Kara karanta wannan

Ana Fama Da Karancin Naira, NSCDC Ta Kama Wasu Gungun Mutane 'Masu Buga Jabun Sabbin Naira Da Daloli'

Gangunan Man Fetur
An kama ganganun man fetur na sata da za a kai Kamaru daga Akwa Ibom. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Yadda aka kama masu satar man fetur din

Imam ya ce sashi masu saka ido kan ruwa na rundunar bayan samun bayanan sirri sun kama wadanda ake zargin a yayin da suke hanyarsu na kai fetur din Kamaru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Sashin ruwa na NSCDC sun kama mutum biyu da ake zargi kuma an kama gangunan fetur a cikin kwale-kwale na kataoko da ruwa a karamar hukumar Ibeno na jihar Akwa Ibom."
"An kama su ne a safiyar ranar Alhamis. Bayan samun bayanan sirri, tawagar NSCDC karkashin jagorancin Jamilu Mohammed Adamu sun bi sahunsu a jirgin ruwa mai inji sun kama kwale-kwalen kusa da tekun Atlantic yayin kokarin shigar da man ta haramtaciyyar hanya zuwa Kamaru."

Kwamandan ya yi gargadin cewa ba za su sassautawa barayin man fetur ba a yankin, yana mai cewa ba za su lamunci duk wani zagon kasa da lalata kayan gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

Ya ce:

"Ba za a cigaba da yadda ake yi a baya ba. Aiki na zo yi a nan, kuma ku yi tsammanin ganin irin hakan domin ba za mu sassauta wa masu satar mai ba da sauran laifuka irinsu."

NSCDC ta kama wasu mutane masu sarrafa jabun dalolin Amurka da sabbin naira a Abuja

A wani rahoton kun ji cewa jami'an NSCDC a birnin tarayya Abuja sun cafke wasu gungun bata gari da ke sarrafa kudaden jabu.

An kama su da jabun dalolin Amurka da sabbin takardun naira na Najeriya da kuma wasu tsaffin kudade bayan samun bayannan sirri a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel