Gobara Ta Tashi a Kasuwar Kayayyakin Gyaran Ababen Hawa a Jihar Legas

Gobara Ta Tashi a Kasuwar Kayayyakin Gyaran Ababen Hawa a Jihar Legas

  • Wata mummunar gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar kayayyakin ababen hawa a ranar Laraba 8 ga watan Maris
  • Ana zargin wasu 'yan daba da kashe wasu mutane a kasuwar kafin daga bisani suka bankawa kasuwar wuta
  • Sai dai, hukumomi sun ce ba kone kasuwar aka yi ba, gobara ce ta tashi daga wani yanki na cikin kasuwar

Jihar Legas - Gobara ta yi kaca-kaca da wani bangare na kasuwar Akere ta kayan ababan hawa da ke yankin Olodi-Apapa a Ajegunle a jihar Legas, inda ta lalata kayayyaki masu darajar miliyoyi.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

A cewar rahoton jaridar Punch, gobarar ta fara ne da misalin karfe 3 na daren Laraba 8 ga watan Maris.

Yadda gobara ta ci kasuwar Legas
Gobarar da ta ci kasuwar Legas | Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

A cewar rahoton, an gano gawar wani mai shekaru 65 da ya rasu a wannan mummunar gobara.

Kara karanta wannan

Babban aiki: NDLEA ta kama 'yan kwaya 793 a Arewa, sun kwato kayan buguwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daraktan hukumar kwana-kwana a jihar Legas, Adeseye Margaret ta fitar da sanarwa a ranar Laraba, inda ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ana zargin wasu da kone kasuwar

Sai dai, rahoton jaridar SaharaReporters na cewa, wasu 'yan daban ne suka zo da misalin karfe 2 na daren Laraba tare da bankawa kasuwar wuta bayan bindige mai gadi.

A wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta, an ji wani yana cewa:

"An harbe mai gadi da wasu mutum biyu har lahira kuma sun tafi binne su nan take."

Shima a nasa bangare, wani babban jami'in Red Cross ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai bayyana ainihin wadanda ake zargi da bankawa kasuwar wuta ba.

Ana yawan samun tashin gobara a kasuwannin Najeriya, musamman a yanayi irin wannan.

Yadda gobara ta yi kaca-kaca da kasuwa a Borno

Kara karanta wannan

Duk Da Ya Lashe Kujerar Sanata a NNPP, Shekarau Ya Ki Karba, Ya Fadi Dalili

A wani labarin, kunji yadda wata mummunar gobara ta yi kaca-kaca da babbar kasuwar jhar Borno a ranar zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.

Wannan lamarin ya tada hankali, inda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana ba da tallafi ga 'yan kasuwar da gobarar ta shafa a jihar.

Hakazalika, gwamnan ya bayyana shirinsa na yin gyara a cikin kasuwar duk dai don ragewa wadanda abin ya shafa radadin rashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel