Akwai Matsala: Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa Ta Sanya Shakku Kan Yiwuwar Ƙidaya a Watan Maris

Akwai Matsala: Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa Ta Sanya Shakku Kan Yiwuwar Ƙidaya a Watan Maris

  • Hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta bayyana shakku kan yiwuwar ƙidayar bana a lokacin da aka tsara
  • Hukumar ta bayyana cewa ɗage zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jihohi da INEC tayi shine ya ɓata mata lissafi
  • Shugaban hukumar yace zai tattauna da shugaban ƙasa domin samo ranar da za a gudanar da ƙidayar ta wannan shekarar

Abuja- Hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta bayyana cewa da kamar wuya a gudanar da ƙidayar shekarar 2023 a cikin watan Maris, kamar yadda aka tsara a baya.

Shugaban hukumar, Nasir Isa-Kwarra, shine ya bayyana hakan yayin wani taro da wakiliyar hukumar asusun ƙidaya na majalisar ɗinkin duniya (UNFPA, Ms Ulla Mueller, ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja. Rahoton Vanguard

Kidaya
Akwai Matsala: Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa Ta Sanya Shakku Kan Yiwuwar Ƙidaya a Watan Maris Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shugaban hukumar ƙidayar ya bayyana cewa yiwuwar ƙin yin ƙidayar baya rasa nasaba da ɗaga zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokokin jihohi da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi ba.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Mamaye Ni Aka Lalube Min Wayoyi Na a Wajen Karɓar Satifiket Ɗin lashe Zaɓe, Sanatan APC

Hukumar INEC a ranar Laraba ta sanar da ɗage zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokokin jihohi wanda aka shirya gudanar wa a ranar Asabar, 11 ga watan Maris, inda hukumar ta ɗage zaɓen zuwa mako guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba dai ƙidayar bana ana tunanin za a fara gudanar da ita ne a ranar 29 ga watan Maris, 2023.

Duk da hakan shugaban hukumar, ya bayyana cewa zai tuntuɓi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin sanya ranar da za a gudanar da ƙidayar ta wannan shekarar.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ko a baya ba a bayyana a hukumance ranar da za a gudanar da aikin ƙidayar ba.

A nata ɓangaren wakiliyar UNFPA, tayi alƙawarin cewa hukumar zata bayar da gudunmawar da ta dace domin ganin an samu gudanar da ƙidayar ta bana cikin nasara. Rahoton The Punch

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Fili, INEC Ta Bayyana Dalilin Dakatar Da Zaɓen Tambuwal Da Sauran Ƴan Majalisun Tarayya a Sokoto

Hukumar ta kuma bayar da manyan kwamfutoci guda sha shida domin gudanar da tattara rahoton bayan aikin ƙidayar.

Jam'iyyar SDP Ta Koma Bayan Ɗan Takarar Gwamnan APC a Jihar Oyo

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Oyo ya samu babban tagomashi, ana dab da zaɓe.

Wata babbar jam'iyyar adawa a jihar ta nuna goyon bayan ta a gare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel