Kotun Koli Ya Maye Gurbin Shekarau da Hanga a Matsayin Dan Takarar Sanatan Kano a NNPP

Kotun Koli Ya Maye Gurbin Shekarau da Hanga a Matsayin Dan Takarar Sanatan Kano a NNPP

  • Kotun koli ya bayyana Sanata Rufai Hanga a matsayin dan takarar sanata a Kano ta tsakiya karkashin inuwar NNPP
  • A baya INEC ta sanar da Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan a jam’iyyar ta NNPP saboda dalilai
  • A baya, Shekarau ya fito daga NNPP tare da komawa PDP, inda yace ba ya yin takara a wannan shekarar

FCT, Abuja - Kotun koli ya tabbatar da Sanata Rufai Hanga a matsayin sahihin dan takarar sanatan jam’iyyar NNPP a Kano ta tsakiya a zaben ‘yan majalisun tarayya da aka yi a ranar 25 ga watan Faburairu.

Wannan na zuwa ne a hukuncin da kotun ya yanke a zamansa da alkalai biyar nasa karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro a ranar Juma’a 10 ga watan Maris, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Yadda Gwamnan CBN Zai Jefa Kan Shi a Cikin Matsala – Shugaban PACAC

Kotun ya ce hukumar zabe ta INEC ta yi kuskuren rashin maye gurbin Sanata Ibrahim Shekarau da Hanga bayan da Shekarau ya yi hijira zuwa jam’iyyar PDP.

An ba Hanga kujerar sanata ta Shekarau
Sanata Rufai Hanga, wanda ya maye gurbin Shekarau | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abin da hukuncin kotu ya bayyana

Mai shari’a Emmanuel Agim a takardar hukuncin da ya karanta wacce mai shari’a Uwani Abba-Aji ta rubuta ta yi watsi da abin da INEC ta gabatar a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ya tabbatar da hukunci biyu da babban kotun tarayya da na daukaka kara da ke Abuja suka yanke na tabbatar da Hanga a matsayin dan takarar NNPP.

A watan Satumban da ta gabata ne Shekarau ya bayyana sauya sheka daga jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso zuwa jam’iyyar PDP.

Yadda lamarin ya faro

Kafin barinsa NNPP, Shekarau ya tsaya takara a jam’iyyar NNPP a lokacin da suke dasawa dan takarar shugaban kasa Rabiu Kwankwaso, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Fadi Abin da Ya Taimaki Bola Tinubu, Ya Doke Atiku Abubakar da Obi

Duk da haka, a ranar 8 ga watan Maris hukumar zabe ta alanta Shekaru din a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a mazabar Kano ta tsakiya.

Abin da ya ja hankalin duniya shine, Shelarau ya bayyana karara cewa ba ya yin takara a NNPP tun da ya fice daga cikinta.

Rahoto ya bayyana cewa, INEC ta ce ya samu kuri’u 456,787 a mazabar ta Kano ta tsakiya a zaben da ya gabata.

A bangare guda, an tumbuke sunan dan majalisar Kano, Ado Doguwa daga jerin wadanda suka lashe zabe a bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel