DHQ: Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 200, Sun Ceto Mutane 161 da Aka Sace a Najeriya

DHQ: Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 200, Sun Ceto Mutane 161 da Aka Sace a Najeriya

  • Dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 216 kuma sun kama wasu miyagu 332 a samame daban-daban a faɗin ƙasar nan cikin mako ɗaya
  • Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a
  • Ya ce sojojin sun kwato manyan makamai iri daban-daban tare da ceto mutum 161 da aka yi garkuwa da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce sojojin kasar nan sun kashe 'yan ta'adda 216 tare da kama miyagu 332 a cikin makon da ya gabata.

Dakarun sojojin sun kuma ceto mutane 161 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan, kamar yadda rahoton The Nation ya kawo.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe ƴan bindiga, sun ƙwato miyagun makamai a jihohin Arewa 3

Sojojin Najeriya.
DHQ ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu a makon jiya Hoto: Defence HQ Nigeria
Asali: Twitter

Mai magana da yawun DHQ na ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kwato miyagun makamai

Janar Buba ya ce sojojin sun kwato makamai iri-iri 234 da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 131, bindigar PKT 3, bindigar M16 guda daya, bindigar gida guda 43, bindigogin Danish 21 da bindigar 105mm guda daya.

Sauran makaman da aka kwato sune bindigogi hannu fistol 18, bindigogi masu sarrafa kansu guda biyu, bam LG4 daya, MG daya, harsashin fashewar abubuwa guda uku da Mowag APC daya.

Kakakin DHQ ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun kwato alburusai kala daban-daban guda 5,994 da sauran makamai masu haɗari daga hannun miyagu a makon jiya.

Nasarorin sojoji a Neja Delta

Da yake jawabi kan ayyukan sojoji a yankin Neja Delta, Buba ya ce sojojin sun kwato lita 533,127 na danyen mai da aka sace da kuma lita 24,520 na dizal da aka tace ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Jam'iyyar PDP ta tsayar da dan takarar gwamna da zai kara da Aiyedatiwa

Bugu da ƙari, sojojin ba su tsaya iyakar nan ba sun kuma kama ɓarayin man fetur mutum 24, rahoton Vanguard.

Kakakin rundunar tsaron ya ce sojojin za su ci gaba da kai hare-hare masu karfi kan 'yan ta'adda ba kakkautawa har sai zaman lafiya ya dawo a ƙasar nan.

"Babu makawa zamu kakkaɓe ta'addanci tare da kawo ƙarshen dukkan ƴan ta'adda maimakon mu tsaya muna durƙusa musu," in ji shi.

Tankoki sun fashe a Ribas

A wani rahoton kuma Motoci aƙalla 100 ne suka ƙone yayin da wasu tankokin fetur suka fashe a cunkoson ababen hawa a titin Gabas-Yamna a Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun maƙale a cikin motocinsu amma har yanzu ba a gano adadin da suka mutu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel