Bayan Cece-Kuce da Ya Biyo Baya, Kotu Ta Baiwa Tinubu Damar Duba Kayan Aikin Zabe

Bayan Cece-Kuce da Ya Biyo Baya, Kotu Ta Baiwa Tinubu Damar Duba Kayan Aikin Zabe

  • Kotun daukaka Kara ya ba Tinubu damar bincika takardun da INEC ta yi amfani dasu a zaben bana na shugaban kasa
  • Kotun ya ba Atiku da Obi damar bincika irin wadannan takardun don samun makama a karar da za su shigar
  • An yi zabe a Najeriya, 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP da Labour sun ce basu amince da sakamakon ba

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara ya ba zababben shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmad Tinubu damar bincika kayan aikin da hukumar zabe ta INEC ta yi amfani dasu a zaben 25 ga watan Faburairu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Tinubu na APC ya bayyana bukatarsa a gaban kotun daukaka karan a ranar Talata cewa, yana son a bashi damar ganin kayayyakin da INEC ta yi aiki dasu a zaben.

Kara karanta wannan

Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

Tinubu ya shigar da bukatar ne ta hannun lauyansa, Mr Akintola Makinde, inda ya ce yana bincika kayayyakin, kana ya samu kwafinsu don kare kansa a gaban kotu.

Tinubu ya samu damar duba takardun aikin zaben bana
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

PDP da APC sun tafi kotu don kalubalantar sakamakon zabe

Idan baku manta ba, ‘yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun Labour da PDP sun ce basu amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karar Tinubu ta farko a ranar 6 ga watan Maris na dauke da sunan dan takarar shugaban kasa na Labour Peter Obi a matsayin wanda ake kara, Vanguard ta ruwaito.

A kara ta biyu, Tinubu ya maka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku da kuma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Dalilin da yasa Tinubu ke neman bayanan zaben bana

A cewar Makinde:

“Kayayyakin za su amfane mu wajen taimaka mana mu shirya yadda za mu kare kanmu da kuma ba mu damar kwantata bayanan da ke ajiye a ma’ajiyar bayanai ta INEC.”

Kara karanta wannan

Afenifere Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Bayyana Dan Takarar Da Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Da suke yanke hukunci a ranar laraba, alkalai uku na kotun daukaka kara sun ce, sun ba Tinubu damar duba bayanan, duk da cewa an dakile shi daga wasu bukatun da aka gabatar.

Idan baku manta ba, kotun a baya ya ba Atiku da Obi irin wannan daman domin samun damar kalubalantar sakamakon zaben da aka yi na shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel