Gidajen Mai Da Ƴan Kasuwa Na Cigaba Da Ƙin Karɓar Tsofaffin Kuɗi

Gidajen Mai Da Ƴan Kasuwa Na Cigaba Da Ƙin Karɓar Tsofaffin Kuɗi

  • Mutane sun watsawa bankunan da suke bayar da tsofaffin kuɗi ƙasa a ido inda suka daina karɓa
  • Masu gidajen mai, motocin haya da sauran ƴan kasuwa dai sun ƙi karɓar tsofaffin kuɗin duk da umurnin kotu
  • Sun bayyana dalilin cewa har yanzu hukumomin da yakamata su sanya su karɓar tsofaffin kuɗin ba su ce komai ba

Sabon yunƙurin da bankuna suka yi na sake fito da tsofaffin kuɗin N500 da N1000 ya samu koma baya a ranar Talata, yayin da masu motocin haya, gidajen mai, masu shaguna da sauran mutane suka ƙi karɓar tsofaffin kuɗin.

Hakan na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 48 bayan wasu bankuna irin su Guaranty Trust Bank Plc, Zenith Bank Plc da Sterling Bank, suka fara bayar da tsofaffin kudin N500 da N1,000 a rassan su dake manyan biranen ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Naira: Gwamnan APC Ya Fusata, Ya Faɗi Babban Laifin Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin N500 da N1000

Tsaffin kuɗi
Gidajen Mai Da Ƴan Kasuwa Na Cigaba Da Ƙin Karɓar Tsofaffin Kuɗi Hoto: Naija News
Asali: UGC

Sai dai binciken da jaridar PUNCH tayi a ranar Talata, ya bayyana cewa tuni wasu mutane suka fara ƙin karɓar tsofaffin takardun kuɗin na N500 da N1,000.

Da yawa daga cikin su, na kafa hujja da cewa har yanzu babban bankin Najeriya (CBN) bai amince da a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin in banda N200.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu gidajen mai a ranar Talata sun ƙi karɓar kuɗin daga hannun mutanen Abuja, Nasarawa da jihar Niger, inda suka haƙiƙance cewa har yanzu bankuna ba suce musu su karɓi kuɗin ba.

Bayan gidajen mai, mafiya yawa daga cikin masu shaguna a biranen har yanzu basu fara karɓar tsofaffin kuɗin ba.

Sakataren ƙungiyar masu siyar da man fetur mai zaman kanta ta Abuja-Suleja, Muhammed Shu'aibu ya bayyana cewa:

“Muna jiran umurnin shugaban ƙasa ne. Har yanzu shugaban ƙasa bai ce komai ba. Sai dai, idan bankunan suka ce mu karɓi tsofaffin kuɗin to tabbas zamu karɓa."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mayaƙan Boko Haram Tsagin ISWAP Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno

Ko a jihohin Legas da Ogun, ma haka abin yake inda gidajen mai da dama da masu motocin haya suka ƙi karɓar tsofaffin kuɗin.

Jaridar Punch ta samo cewa an samu hatsaniya sosai a tsakanin masu sayar da mai a gidajen mai da masu motoci akan tsofaffin kuɗin N500 da N1000.

Kwastomomin da suka je siyan mai da tsofaffin kuɗin sun rasa madafa domin an ƙi a basu man fetur ɗin.

Masu Sayar Da Hatsi a Kasuwannin Abuja Bayyana Dalilin Da Yasa Ba Su Karban Tiransifa, Sai Tsabar Kudi

A wani labarin na daban kuma, masu sana'ar hatsi a kasuwannin Abuja sun bayyana dalilin su na ƙin karɓar tiransifa sai tsabar kuɗi.

Ƙarancin kuɗi a hannun mutane dai ya sanya dole aka rungumi harkar tiransifa domin harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel