Yanzu Yanzu: Mayaƙan Boko Haram Tsagin ISWAP Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno

Yanzu Yanzu: Mayaƙan Boko Haram Tsagin ISWAP Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno

  • Yan Boko Haram na cigaba da zafafa hare hare a ƙoƙarin da suke na cusa tsoro a zuƙatan mutane
  • Duk da ƙalubale da suke fuskanta, suna kawar da hankalin mutane domin nuna har yau suna da ƙarfi ta hanyar kai hare hare
  • Sun ƙaddamar da hari akan babura, ta hanyar harbin kan mai uwa da wabi, sun kashe masunta 26 tare da jikkata gommai

Borno - A yayin da faɗa ke tsamari tsakanin Boko Haram tsagin Shekau da kuma ISWAP, ayyukan Mayaƙan na cigaba da ta'azzara sosai.

Hakan baya rasa nasaba da yadda suke samun koma baya wajen makamai, abinci da kuma yawan adadin su.

Dalili kenan da yasa suke ƙara kai hare-hare da sace-sacen mutane domin ƙara jefa tsoro a zuciyar mutane da kuma samun kuɗin gudanar da ayyukan su haramtacce.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Ƙasa Yayi Taho Mu Gama Da Wata Mota a Legas, Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata

Iswap
Yanzu Yanzu: Mayaƙan Boko Haram Tsagin Iswap Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno Hoto: UGC
Asali: Twitter

Hakan ce tasa a ƙalla masunta 26 ƙungiyar ta kashe a yayin wani ƙaddamar da hari da ISWAP din takai a garin Gamborun Ngala dake bornon Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Leadership ta ruwaito cewar, masuntan suna tsaka da gudanar da sana'ar su ta kama kifine, kawai sukaji maharan sunyi musu dirar mikiya tare da harbi takan mai uwa da wabi.

Wasu daga cikin maharan sunji aman wuta ne yayinda suke ƙoƙarin samo itace, a can ƙauyen Mukdolo dake kilomita 19 arewacin garin Dikwa na jihar Borno.

Zagazola Makama, masani a ɓangaren hare haren taaddancin dake gudana a tafkin Chadi yace, maharan sun dimfari wajen ne akan babura masu yawa, tare da ƙaddamar da hari ta hanyar harbin kan mai uwa da wabi.

Majiyar tamu bata tsaya anan ba, tace 9 daga cikin waɗanda aka ƙaddamar wa da harin sun samu tsira, uku daga ciki na ɗauke da mummunan harbin harsashi , yayin da sauran da aka ƙaddamar musu, tuni suka ce ga garin ku nan.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Fili, INEC Ta Bayyana Dalilin Dakatar Da Zaɓen Tambuwal Da Sauran Ƴan Majalisun Tarayya a Sokoto

A cewar majiyar:

"Suna zuwa, suka ce su kwanta. Daga nan sai suka yi amfani da ragar kama kifin su, suka ɗaure su dashi. Daga nan suka ci gaba da yi musu azaba. Bayan sun fita daga hayyacin sune, sai suka buɗe musu wuta, nan take suka sheƙa barzahu".

Sauran jikkunan mamatan guda 26 an same sune , ta hanyar bincike da akayi cikin jagorancin waɗanda suka tsira, lokaci ƙadan bayan maharan sun gama aiwatar da ta'annatin sun bar wajen.

Ana Daf Da Zabe, Yan Bindiga Sun Kona Gidan Dan Takarar PDP Da Na Mahaifinsa

Wasu yan bindiga da ba a tabbatar ko su wanene ba sun tafi gidan dan takarar majalisar jiha karkashin jam'iyyar PDP sun cinna wa gidan wuta.

Maharan basu tsaya nan ba sun kuma tafi gidan mahaifin dan takarar nan ma sun banka wa gidan wuta suka jira sai da komai ya kone kurmus kafin suka tatattara kayansu suka tafi.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Garzaya Kotu, Peter Obi Ya Aikewa Magoya Bayansa Da Wani Muhimmin Gargaɗi

Dan siyasar da kansa ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai nuna bakin ciki da bacin rai duk da cewa babu wanda ya rasa rai sakamakon harin, ya yi kira ga kwamishinan yan sandan jihar ya yi bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel