Jiragen Yaƙin Sojin Sama Sun Halaka Wata Mata Mai Juna Biyu a Kaduna

Jiragen Yaƙin Sojin Sama Sun Halaka Wata Mata Mai Juna Biyu a Kaduna

  • Jiragen yaƙin sojojin saman Najeriya sun halaka wata mata mai ɗauke da juna biyu da wasu ƙananan yara a jihar Kaduna
  • Jiragen yaƙin dai sun biyo wasu ƴan bindiga ne waɗanda suka arce zuwa cikin ƙauyen da lamarin ya auku
  • Matar mai ɗauke da juna biyu ɗa ƙananan yaran da aka halaka a yayin harin duk ƴan gida ɗaya ne

Jihar Kaduna- Hare-haren sama na rundunar sojin saman Najeriya sun halaka wata mata mai juna biyu da wasu ƙananan yara biyu a ƙauyen Sabon Gida na gundumar Fatika, a cikin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Jiragen yaƙin dai sun hari wasu ƴan bindiga ne waɗanda suka rugo zuwa cikin ƙauyen daga wani daji dake makwabtaka da su.

Jirgin yaƙi
Jiragen Yaƙin Sojin Sama Sun Halaka Wata Mata Mai Juna Biyu a Kaduna Hoto: The Witness Nigeria
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta samo cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe biyar na yamma.

Kara karanta wannan

"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

Mamatan dai ƴan gida ɗaya ne sannan akwai kusan wasu mutum biyar a ƙauyen da suka samu raunika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jagora a ƙauyen, Hamisu Kurau, ya tabbatarwa jaridar Daily Trust da aukuwar lamarin ta wayar tarho.

"Jiragen yaƙin wasu ƴan bindiga biyu suke hari waɗanda suka rugo zuwa cikin ƙauyen. Sai dai basu samu ƴan bindigan da suke hari ba, sannan suka halaka matar mai ɗauke da juna biyu, Mai suna Furaira da wasu ƙananan yara biyu a gidan." Inji shi

Ya bayyana cewa mijin marigayiyar mai suna Bala, da mahaifin yaran guda biyu, Muntari, ƴan'uwa ne. Rahoton The Witness

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, domin jin ta bakin sa, sai ya ƙi cewa komai amma ya nemi da a tuntuɓi hukumomin sojin sama.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 Da Ya Wajaba Tinubu Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa

Haka kuma, shi ma kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin yau da kullum na jihar, Samuel Aruwan, bai amsa kiran wayar da akayi masa ba kuma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba kan lamarin.

Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Bijilanti da Dama a Jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun halaka mutane da dama a jihar Kaduna a yayin wani hari da suka kai.

Daga cikin waɗanda suka rasa ran su a harin har da ƴan bijilanti masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel