Dalilin Da Yasa Na Ki Karbar Kujerar Sanatan NNPP – Shekarau

Dalilin Da Yasa Na Ki Karbar Kujerar Sanatan NNPP – Shekarau

  • Sanata Ibrahim Shekarau ya ki zuwa karban takardar shaidar cin zaben sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce shi ba dan jam'iyyar NNPP bane a yanzu don haka ba zai karbi satifiket din cin zabe ba
  • Hukumar INEC dai ta ayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben sanata a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya kauracewa zauren taro na kasa da kasa (ICC) inda zababbun sanatoci suka karbi takardar shaidar cin zabensu a ranar Talata, 7 ga watan Maris.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ayyana Shekarau a matsayin wanda ya yi nasara a zaben Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya karkashin inuwar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Sai dai kuma, dan majalisar mai ci a yanzu bai halarci taron karbar satifiket din cin zaben ba, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: PDP Ta Koka, Ta Ce INEC Na Kokarin Goge Hujja Da Ake Da Shi Kan Nasarar Tinubu

Sanata Ibrahim Shekarau yana murmusawa
Dalilin Da Yasa Na Ki Karbar Kujerar Sanatan NNPP – Shekarau Hoto: Leadership
Asali: UGC

Mai magana da yawun Shekarau, Sule Y. Sule, ya fada ma jaridar Leadership cewa ubangidansa ya rigada ya fito karara ya bayyana cewa ba zai karbi takardar shaidar cin zaben ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Mun rigada mun yi karin haske a kan matsayinmu fame da lamarin. Sanata Shekarau baya da niya kuma ba zai karbi takardar shaidar cin zabe ba. Saboda bin tsari da kuma ra'ayi na kashin kai."

Martanin shugabannin jam'iyyar NNPP

Bayan sanar da Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Kano ta tsakiya, shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufai Alkali ya ce Shekarau ya bar jam'iyyar amma abun takaici, INEC ta dawo da shi a matsayin zababben sanatan Kano ta tsakiya.

Farfesa Alkali ya ce:

"Bai kamata mu yi magana kan wannan ba, amma Shekarau ya yarda da dawowa jam'iyyarmu, mun karbe shi, ya samu tikitin takarar kujerar sanatan Kano, amma daga baya ya rubutawa shugabanmu wasika cewa ya yi murabus daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

"An sake gudanar da zaben fidda gwani inda Sani Hanga ya yi nasara amma INEC bata karbi sunansa ba. mun je kotu sannan muka yi nasara, sun tafi kotun koli.
"INEC ba jam'iyyar siyasa bace, me zai sa ta zuwa kotu? Na san cewa a kotun ra'ayin jama'a, akwai bangaren da'a. Muna a kotun koli kan lamarin Shekarau."

Sai dai kuma, sakataren NNPP, Dr Major Agbo, ya sanar da jaridar cewa Shekarau bai da alaka da zuwa karbar takardar shaidar cin zabe tunda ya bar jam'iyyarsu.

Agbo ya ce:

"Babban abun shine cewa jam'iyyarmu ta yi nasara. Har yanzu lamarin na kotu amma jam'iyyar za ta gabatar da sahihin dan takarar kujerar sanatan Kano ta tsakiya saboda mun aika jerin sunayenmu ga INEC amma basu riga sun aiwatar da shi ba."

Hakan bai dace ba: Kwankwaso ya magantu kan belin da kotu ta ba Ado Doguwa

A wani labari na daban, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah wadai da belin da kotu ta baiwa Alhassan Ado Doguwa bayan zarginsa da ake da kisan wasu magoya bayan NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel