Hukumar INEC Ta Dakatar da Kwamishinan Zabe Na Jihar Sakkwato

Hukumar INEC Ta Dakatar da Kwamishinan Zabe Na Jihar Sakkwato

  • INEC ta dakatar da kwamishinanta na jihar Sakkwato kuma nan take ta maye gurbinsa
  • A wata wasiƙa da ta tura zuwa reshenta na jihar, INEC ta umarci Nura Ali ya miƙa komai hannun Sakatariyar gudanarwa
  • Wani ma'aikaci ya bayyana cewa jinkirin da aka fuskanta a zaben da ya gabata ne suka haddasa ɗaukar wannan matakin

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta dakatar da kwamishinan zabe a jihar Sakkwato (REC), Dakta Nura Ali, kuma matakin zai fara aiki nan take.

Channels tv ta ce hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakataren INEC, Rose Orlaran-Anthony, zuwa ga REC ɗin da Sakataren hukumar na jihar.

Hukumar zabe ta ƙasa INEC
Hukumar INEC Ta Dakatar da Kwamishinan Zabe Na Jihar Sakkwato Hoto: INECNigeria
Asali: Twitter

Wasiƙar ta umarci Dakta Ali ya tattara ya bar Ofishin hukumar INEC da ke jihar Sakkwato, arewa maso yammacin Najeriya, har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Faɗi Aikin da Yake Yayin da Atiku da Jiga-Jigan PDP Suka Fara Zanga-Zanga a Abuja

Haka nan INEC ta umarci Sakatariyar gudanarwa, Hajiya Aliyu Kangiwa, ta maye gurbinsa nan take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan na zuwa ne awanni 48 bayan shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya lashi takobin gano jami'an hukumar masu sakaci da ɗaukar mataki kansu, sai ga shi ya cika kalamansa a aikace.

Meyasa INEC ta dakatar da REC na Sakkwato?

Duk da wasiƙar ba ta ambaci dalilin ɗaukar mataki kan REC ɗin ba, amma wata majiya a INEC ta shaida wa Daily Trust cewa yana da alaƙa da abinda wasu ma'ikatan karkashin Ali suka yi a zaben da ya gabata.

Legit.ng ta tattaro zaben da ya gudana a Sakkwato cike yake da matsaloli da jinkiri, idan aka jingine na shugaban kasa wanda PDP ta samu nasara, sauran an ce ba su kammalu ba har da na Sanatoci uku.

Kara karanta wannan

"Bamu Haɗa Baki da Kowa Ba" INEC Ta Saurari Su Atiku, Ta Faɗi Matakin da Zata Dauka Kan Zaben Shugaban Kasa

Wannan ne karo na farko da Nura Ali ya jagoranci zaɓe tun bayan naɗa shi a matsayin kwamishina a shekarar da ta gabata.

Yayin da yake tsokaci kan ci gaban, majiyar ta ce:

"Kun san an samu jinkiri da dama a zaben da ya gabata, rashin zuwan kayan zaɓe rumfunan kaɗa kuri'a da wuri da rashin baiwa ma'aikatan wucin gadi horo mai kyau."
"Kuma jihar Sakkwato na da wuyar sha'ani a batun zaɓe, tana bukatar gogagge, mai kwarewa. Ruɗanin da ya faru lokacin zaben baya ne babban makasudin dakatar da shi."
"Yanzu an turo tawagar kwararru kuma gogaggu da zasu jagoranci zaben gwamna da sauran zaɓukan da ke tafe a jihar."

Wani babban jami'in INEC da ya nemi a boye sunansa domin ba shi da hurumin magana kan batun, ya ce baki ɗaya ma'aikata a jihar sun bar Nura Ali shi ɗaya saboda salon jagorancinsa.

"INEC ta fahimci cewa REC ɗin Sokoto na aiki kamar shi kaɗai ne mai gudanarwa hakan ya jawo rushewar tsarin gudanarwa na hukumar a Sakkwato."

Kara karanta wannan

Ainihin Dalilan da Suka Jawo APC Ta Ji Kunya a Legas, Kaduna, Katsina da Jihohi 9

"Alal misali, har yanzu babu sakamakon zaben majalisar tarayya ko ɗaya daga jihar sakamakon ma'aikatan sun ƙaurace masa saboda ya riƙe komai," inji shi.

Wike Ya Fadi Abinda Yake Yi Yayin da Atiku da Jigan-Jigan Ke Zanga-Zanga

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya yi wa Atiku da sauran shugabannin PDP Shagude game da zanga-zangar da suka yi a Hedkwatar INEC

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce girman kai da rashin jin gargaɗin G-5 ya jawo wa jam'iyyar PDP da shugabanninta wannan halin.

Wike ya ce yayin da su Atiku suka tsunduma zanga-zangar adawa da sakamakon zabe, shi kuma ya maida hankali ne kan zuba wa mutanensa ayyukan da zasu gode.

Asali: Legit.ng

Online view pixel