Wani Matashi Ya Fara Tattaki Akan Keke Daga Katsina Zuwa Legas Domin Taya Tinubu Murna

Wani Matashi Ya Fara Tattaki Akan Keke Daga Katsina Zuwa Legas Domin Taya Tinubu Murna

  • Wani matashi bakatsine ya fara tattaki daga Katsina zuwa jihar Legas domin taya Tinubu murna
  • Matashin ya bayyana cewa tun kafin a kammala sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ya fara tattakin sa
  • Bakatsinen matashin wanda yake tattakin a keke ya bayyana dalilin da ya sanya yake yin tattakin nasa

Jihar Kwara- Wani matashi ɗan shekara 26 a duniya mai suna Gaddafi Musa, ya fara tattaki akan keke daga jihar Katsina zuwa jihar Legas domin taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, murnar lashe zaɓen da yayi. Rahoton The Nation

A cewar shafin distance calculator.net a manhajar bincike ta Google map search, nisan Katsina zuwa Legas ya kai kilomita 1,227 akan hanyar mota.

Tattaki
Wani Matashi Ya Fara Tattaki Akan Keke Daga Katsina Zuwa Legas Domin Taya Tinubu Murna Hoto: The Nation
Asali: UGC

Musa, wanda ya isa Ilorin, babban birnin jihar Kwara, jiya da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, yace ya fara tafiyar sa ne ranar Laraba, lokacin mafiya yawan jihohi sun miƙa sakamakon zaɓen su, bayan alamu sun nuna cewa Tinubu zai lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Firaministan Ingila Yayi Magana Kan Nasarar Tinubu, Yayi Masa Wani Muhimmin Alƙawari

A cewar sa ya fara wannan tattakin ne domin ya cika alƙawarin da ya ɗauka na taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar murna akan keken sa har cikin gidan sa a birnin Legas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Musa ya bayyana cewa duk da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bai san shi ba, ya yanke shawarar yin wannan tafiya saboda yana sane sa nasarorin da ya samu lokacin yana gwamnan jihar Legas. Rahoton Radio Nigeria Kaduna

“Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tallafawa ƴan gudun hijira da waɗanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su a lokuta da dama da maƙudan kuɗaɗe, da ziyartar su, domin rage musu raɗaɗin da suke ciki." Inji shi
"Tinubu ya kai ziyar jihar Borno kusan sau uku, domin jajantawa ƴan gudun hijira da taimaka musu da kuɗaɗe. Ina yabawa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bisa ƙaunar da yake nunawa kowa ba tare da yin la'akari da addini ko ƙabila ba."

Kara karanta wannan

"Na Daina Yin Zaɓe" Matashi Ya Fusata Ya Jefa Katin Zaɓen Sa Cikin Bola, Bidiyon Ya Yaɗu

Musa yace yana fara tafiyar sa ne a kan keken sa daga ƙarfe shida na safe zuwa shida na yamma saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan.

Ya roƙi ƴan Najeriya da su goyawa zaɓaɓben shugaban ƙasar baya domin ya samu nasara.

Idan Aka Zabe Ni, Zan Fara Ba Matasan Delta N30,000 Duk Wata, Inji Dan Takarar Gwamna Na SDP

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Delta ya yiwa matasan jihar wani muhimmin alƙawari.

Ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar SDP yace zai riƙa ba matashi wasu kuɗaɗe duk wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel