Tashin Hanakali Yayin da Wakilin PDP Ya Yanki Jiki Ya Fadi Matacce a Wurin Tara Sakamakon Zabe

Tashin Hanakali Yayin da Wakilin PDP Ya Yanki Jiki Ya Fadi Matacce a Wurin Tara Sakamakon Zabe

  • Labarin da muke samu daga jihar Benue ya bayyana cewa, wani jigon PDP ya yanki jiki ya fadi matacce a wurin tattara sakamakon zabe
  • Wannan lamarin ya faru ne a karamar hukumar Katsina Ala ta jihar, yanki mai fama da rikicin 'yan bindiga da masu satar mutane
  • Ya zuwa yanzu, majiya daga dangin mamacin ta tabbatar da rasuwarsa, ta kuma bayyana yadda aka yi ya rasu

Jihar Benue - Wani wakilin jam’iyyar PDP a gundunar Mbacher a karamar hukumar Katsina Ala, Hon. Enouch Mson Atsehe ya yanki jiki ya fadi matacce a wurin tattara sakamakon zaben karamar hukumar.

An ruwaito cewa, mamban na PDP dan asalin gundumar Mbacher ne, gunduma mafi girma a karamar hukumar Katsina Ala da ke jihar Benue.

Amma saboda baranazar tsaro, an mayar da cibiyar tattara sakamakon zaben yankin zuwa garin Katsina Ala a madadin gundumar mafi girma.

Kara karanta wannan

Sakamakon Kano: Kwankwaso Ya Lallasa Bola Tinubu a Karamar Hukumar Gwamna Ganduje

Yadda wakilin PDP ya rasu a Benue
Taswirar jihar Benue a Arewacin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Dangi ya tabbatar da mutuwar wakilin PDP

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kawunsa, tsohon kwashinan kasuwanci da masana’antu na jihar, Gon, Terfa Ihidan ya tabbatar da rasuwar jigon na PDP ga jaridar The Nation.

Ya shaidawa jaridar cewa, dangin nasa ya rasu ne bayan da ya ce zai fita domin yin uzuri a wurin tattara kuri’un.

Marigayi Atsehe ya fito ne daga gundumar Mbacher, Shitile a karamar hukumar Katsina Ala. Ya rasu ya bar mata da yara da dangi mai mai yawa.

Har yanzu ana ci gaba da tattara zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Najeriya, a wasu wuraren an samu tashin hankali daga 'yan daba.

An samu munanan yanayi a wasu jihohin, inda aka farmaki ma'aikatan zabe da masu kada kuri'un da suka yi zaben jiya.

An kone akwatin zabe a jihar Edo

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Guguwa: Jam'iyyar Labour Ta Kawo Karshen Mulkin Dan Majalisa Bayan Zango Hudu A Kaduna

A wani labarin, kunji yadda wasu 'yan daba suka kone akwatunan zabe a wata rumfar zabe da ke Benin a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.

Rahoto ya bayyana cewa, 'yan daban sun gano an fi kada wa Obi kuri'a ne, hakan ya basu takaici suka farmaki masu kada kuri'u a rumfar.

Mazauna yankin sun ce ko yanzu aka sake basu dama Peter Obi za su zaba a wannan zaben da aka kammala a jiya Asabar a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel