Bidiyon Yadda Ake Amfani da Fitila a Wurin Kada Kuri’a a Wata Rumfar Zabe Ta Jihar Bauchi

Bidiyon Yadda Ake Amfani da Fitila a Wurin Kada Kuri’a a Wata Rumfar Zabe Ta Jihar Bauchi

  • Wani bidiyo ya nuna lokacin da ake ci gaba da kada kuri'a har kusan karfe 9 na daren ranar Asabar 25 ga watan Faburairu
  • Jama'a a jihar Bauchi sun yi amfani da fitilar wayoyinsu domin tabbatar da sun dangwala kuri'unsu a zaben bana
  • An samu hargitsi a wasu bangarorin Najeriya, musamman Kudancin kasar a inda aka sace na'urorin tantance masu kada kuri'u

Jihar Bauchi - Aikin zabe ya kai dare a makarantar firamaren Unguwar Galadima da ke jihar Bauchi, an ga jami'an zabe na aiki har kusan karfe 9 na dare.

A wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta ta Facebook, an ga lokacin da masu kada kuri'un da kuma turawan zabe ke amfani da hasken fitila a wurin kada kuri'un.

A cikin bidiyon, ga maza da mata na tsaye, inda kowa ke kokarin ganin ya kada kuri'arsa kamar yadda ya zama 'yancin kasa su zabi shugabanninsu a zabe irin wannan.

Kara karanta wannan

Karin bayani: INEC ta dage zaben shugaban kasa a rumfuna 141 na wata jiha

Inda aka kada kuri'u a jihar Bauchi
Inda aka kada kuri'a da dare a Bauchi | Hoto: Usman M A Karofi
Asali: Facebook

A bayyana ne yake, makarantar da ake kada kuri'un babu wutar NEPA ko wata hanyar haske face su yi amfani da fitilun wayoyinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, za a rufe kada kuri'u ne da misalin karfe 2:30 na rana, tare da fara kirge nan take.

An samu tashin hankali a wasu rumfunan zabe

A wasu yankunan kuma a Najeriya, an samu tashin hankali, inda 'yan daba suka sace na'urorin da ake amfani dasu don tantance masu kada kuri'u.

Daga cikin inda wannan lamari mara dadi ya faru akwai jihar Katsina, inda aka sace na'urori shida, amma an kwato uku.

Hakazalika, makamancin lamarin ya faru a jihar Delta, inda nan ma aka sace wasu na'urorin a lokacin da ake tsaka da aiki.

An farmaki jami'an EFCC a jihar Imo da Abuja

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Ta'adda Sun Kai Kazamin Hari Kan Masu Kaɗa Kuri'a a Borno

A wani labarin kuma, kun ji yadda wasu 'yan daba suka farmaki jami'an hukumar EFCC a birnin tarayya Abuja.

Halazalika, sun hari jami'an hukumar a jihar Imo da ke Kudancin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An samu tashe-tashen hankula wasu wurare daban-daban a zaben bana na 2023 a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel