Mutane Sun Yi Takansu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Kai Hari a Jihar Borno

Mutane Sun Yi Takansu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Kai Hari a Jihar Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari garin Goza a jihar Borno yayin da mutane ke kan layi don a tantance su
  • Sarkin Goza, Mohammed Shehu Timta, yace mutane 5 sun ji raunuka a harin kuma an tafi da su Maiduguri
  • Tuni dai jami'an tsaro suka kai ɗauki kuma suka fatattaki maharan, a halin yanzu an ci gaba da zabe

Borno - Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki garin Goza, ƙaramar hukumar Goza a jihar Borno ranar Asabar, sun tarwatsa wurin zaɓe.

'Yan ta'addan sun kutsa kai cikin garin ne yayin da masu kaɗa kuri'a ke kokarin sauke nauyinsu a zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya wanda ke gudana yau.

Taswirar jihar Borno.
Mutane Sun Yi Takansu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Kai Hari a Jihar Borno Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Sarkin Goza, Mohammed Shehu Timta, ya tabbatar da kai harin ga jaridar Daily Trust, inda ya bayyana cewa mutane 5 suka ji raunuka.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sakamakon Zaben Akwatin Atiku Ya Fito, Ya Lallasa Tinubu da Kwankwaso

Sarkin ya ce

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ƙungiyar Boko Haram ta kawo mana hari har cikin kwaryar gari, suka bude wuta kan mai uwa da wabi, mutane 5 suka ji raunuka kuma tuni aka garzaya da su Asibiti a Maiduguri domin kula da lafiyarsu."
"Sun shigo da karfe 8:30 na safe, lokacin masu kaɗa kuri'u sun yi layi domin fara tantance su, da yawan mutanen da suka tsere daga Rumfunan zabe ba su dawo ba amma muna kokarin jawo hankalinsu su dawo su jefa kuri'a."

Basaraken ya ƙara da cewa cikin kankanin lokacin jami'an tsaro suka kawo ɗauki kuma suka yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan.

"Mataimakin Sufetan yan sanda na kasa mai kula da shiyyar arewa maso gabas, wanda ɗan aslin Goza ne, yana nan tare da mu kuma komai a dawo daidai a halin yanzu," inji Sarkin.

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Fasa Akwatunan Zabe, Yan Sanda Sun Tarwatsa Kowa Da 'Tear Gas'

Garin Goza mahaifa ce ga ɗaya daga cikin Sanatocin ɗa suka yi fice a Najeriya, Sanata Ali Ndume, wanda ke neman sake komawa majalisar dattawa a zaben yau.

Sai dai babu tabbacin ko Sanata Ndume na garin domin kaɗa kuri'arsa a zaben shugaban ƙasa da yan Majlisun tarayya da ke ci gaba da gudana, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Enugu Ya Tsallake Rijiya da Baya

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Farmaki Ayarin Ɗan Takarar Gwamnan APC, Sun Bude Wa Motar da Yake Ciki Wuta

Wank ganau ya ce motar sulken da ɗan takarar ke ciki ne ta cece shi amma yadda suka bude masa wuta da yanzu wani labarin ake daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel