Kotun Koli Ya Dage Ci Gaba da Sauraran Karar Gwamnoni da Gwamnatin Tarayya

Kotun Koli Ya Dage Ci Gaba da Sauraran Karar Gwamnoni da Gwamnatin Tarayya

  • Kotun koli ya ba dage ci gaba da zaman karar su El-Rufai kan gwamnatin tarayya da kuma bankin CBN
  • An ce a ranar 3 ga watan Maris ne za a ci gaba da saurarar karar, duk da kuwa kotun ya sha alwashin daddale komai a yau
  • CBN ya ce akwai kudi a kasa, amma bankuna sun ki zuwa su dauka don rabawa mutane kudin

FCT, Abuja - Bayan sauraran batutuwa, kotun koli ya yanke sake zama a shari'ar gwamnoni da gwamnatin tarayya, rahoton Daily Trust.

Wasu gwamnoni a Najeriya sun maka gwamnatin tarayya a kotun koli game sabuwar dokar Naira.

Gwamnonin na neman kotu ta tabbatar da tsawaita wa'adin daina amfani da tsoffin kudi.

A yau aka yi zama na uku, kuma kotun ya sake tura ci gaba da sauraran shari'ar zuwa 3 ga watan Maris mai zuwa.

Kara karanta wannan

Wa ya kaiku: Yadda aka maka matasa a kotu saboda fasa kofar Shoprite a wata jiha

An dage ci gaba da sauraran karar kudi
Yadda wa'adin kudi ya shafi jama'a, gwamnoni suka sa CBN a kotu | Hoto: Davd Darius
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda batun yake a tun farko

Idan baku manta bam gwamnatin Najeriya ta kirkiri sabbin Naira tare da ba da umarnin a daina amfani da tsoffin N200, N500 da kuma N1000.

Wannan lamari ya zo da tsaiko, domin kuwa an gaza samun sabbin kudaden da aka buga, ga kuma tsoffi sun shiga bankuna sun gaza fita, kana wa’adin ya yi kunci.

Hakan yasa wasu gwamnonin kasar nan suka shiga kotun koli domin tabbatar da an tsawaita wa’adin dain amfani da tsoffin kudaden.

Wadanda suka kai Buhari kotu

Daga cikin wadanda suka shigar da karar a farko sun hada da gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara, wasu gwamnoni daga baya sun shiga jerin masu kara, wasu kuma jerin wadanda ake kara, Punch ta ruwaito.

An yi zaba a baya tare da ba da umarnin a ci gaba da karbar tsoffin kudin har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu, amma aka saba umarnin.

Kara karanta wannan

Assha: EFCC ta kame daraktan kamfen gwamnan PDP na Arewa da kudade a hanyar zuwa zabe

Hakazalika, an sake zama tare da sanya ranar 22 ga watan don ci gaba da zama, a yau kuma aka sake dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Maris mai zuwa.

Akwai kudi a kasa, CBN magantu

A gefe guda, CBN ya ce akwai wadatattun kudaden da ya buga kuma yana ba dukkan bankuna su raba a kasar.

Ya kuma shaida cewa, bankuna ba sa zuwa daukar sabbin kudi, don haka kudin suka gaza shiga hannun mutane.

Ya zuwa yanzu dai gwamnati da bankuna na ci gaba da ganin laifin juna kan karancin sabbin Naira da ake fama dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel