Murja Kunya: An Koma Kotu Yau , Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku

Murja Kunya: An Koma Kotu Yau , Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku

  • Bayan yan kwanaki tsare a gidan yari, an sake gurfanar da Murja Kunya gaban kotu a jihar Kano
  • Hukumar yan sanda ta damke Murja ne yayinda take shirin bikin ranar haihuwarta a jihar Kano
  • Alkalin kotun a karo na biyu bai bada belinta ba, ya ce a cigaba da tsareta a gidan gyara hali

Kano - A yau Alhamis, 16 ga watan Febrairu, shahrarriyar yar dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta sake gurfana gaban kotun shari'ar Musulunci dake Filin Hoki jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya.

Arewa Radio ta ruwaito cewa Alkali Mai Shari'a yayi umarni a maida Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali da tarbiyar zuwa mako guda.

Murja dai har ila yau ta musanta tuhumar da ake yi mata a gaban kotu.

Murja
Murja Kunya: An Koma Kotu Yau , Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku Hoto: Freedom Radio
Asali: Facebook

Freedom Radio ta ruwaito cewa game da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba.

Kara karanta wannan

An shiga firgici yayin da mata mai tabin hankali a Kano ta jefa jaririyarta a masai

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.

Damke Murja Ibrahim Kunya

A farkon watan nan, an gurfanar da shahrarriyar Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya gaban Kotun shari'ar Muslunci dake Filin Hoki a jihar Kano.

Ta gurfana ne ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

An karanto mata tuhumar da ake mata inda nan take ta musanta, daga nan ne kuma lauyanta, Barrister Yasir Musa, ya nemi a bada belinta.

Alkali mai Shari'a Abdullahi Halliru ya yi watsi da wannan bukata na lauyan Murja Ibrahim Kunya kuma ya bada umurnin jefa ta gidan ajiya da gyaran hali.

Lauyan Murja ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari amma Alkalin kotun ya sake watsa masa kasa a ido.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Abokan Murja Kunya Bisa Yada Batsa Ta Shafin TikTok

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel