An Gurfanar da Murja Kunya Gaban Kuliya, Tace Karya Ake Mata

An Gurfanar da Murja Kunya Gaban Kuliya, Tace Karya Ake Mata

  • Bayan damke a karshen makon da ya gabata, Murja Ibrahim Kunya ta gurfana gaban kotun sharia
  • Murja wacce ta shahara da zage-zage a kafafen sada zumunta ta shiga hannun hukuma ne bisa kararta da kawayenta suka shigar kanta
  • Alkalin kotun ya ki amincewa da dukkan bukatun lauyoyinta kuma yace a ajiyeta a gidan gyara hali

Kano - An gurfanar da shahrarriyar Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya gaban Kotun shari'ar Muslunci dake Filin Hoki a jihar Kano a yau Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

An karanto mata tuhumar da ake mata inda nan take ta musanta, daga nan ne kuma lauyanta, Barrister Yasir Musa, ya nemi a bada belinta, rahoton Freedom Rediyo.

Kara karanta wannan

Kaico: An gurfanar da matashi a Arewa bisa zargin satar hula da kayan sakawa

Alkali mai Shari'a Abdullahi Halliru ya yi watsi da wannan bukata na lauyan Murja Ibrahim Kunya kuma ya bada umurnin jefa ta gidan ajiya da gyaran hali.

Murja
An Gurfanar da Murya Kunya Gaban Kuliya, Tace Karya Ake Mata Hoto: Freedom Radio Nigeria
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Murja ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari amma Alkalin kotun ya sake watsa masa kasa a ido.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2023.

Kano: Rundunar 'Yan Sanda Tace Za a Gwada Kwakwalwar Murja Kafin a Cigaba da Bincikarta

Rundunar 'yan sandan jihar Kano tayi umarnin fara yi wa Murja Ibrahim Kunya, fitacciyar 'yar TikTok da suka kama a jihar, gwajin kwakwalwa da farko don gane ko hankalinta daya.

Mamman Dauda, kwashinan 'yan sandan jihar ne ya bada wannan umarnin kamar yadda SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Kiyawa ya sanar da cewa, sai har an gudanar da gwajin kwakwalwar kan matashiyar mai shekaru 24 kafin 'yan sandan su cigaba da bincike.

A ranar Lahadi ne dai runduna 'yan sandan jihar Kano suka yi ram da Murja Ibrahim Kunya bayan sun samu korafi kan yadda ta ke zage-zage tare da bata tarbiya a dandalin sada zumunta na TikTok.

An yi caraf da Murja a fitaccen otal na Tahir Guest Palace da ke birnin yayin da ta ke shirin gagarumin shagalin bakin ranar zagayowar haihuwarta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel