Abin Tausayi Yayin da Mata Mai Fama da Tabin Hankali Ta Jefa Jaririyarta a Masai a Jihar Kano

Abin Tausayi Yayin da Mata Mai Fama da Tabin Hankali Ta Jefa Jaririyarta a Masai a Jihar Kano

  • Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta bayyana yadda ta ceto wata jaririya da aka tsoma a masar a jihar
  • Mahaifiyar jaririyar ce ta jefa yarinyar a masai, an ce mahaifiyar na da tabin hankali, dalilin yin haka kenan
  • A wani labarin, wata budurwa ta yi tattaki a Kano domin gano inda saurayinta yake da kuma dawo dashi gida

Jihar Kano - Jami’an hukumar kashe gobara a jihar sun ceto wata jaririya da mahaifiyarsa mai tabin hankali ta jefa a masai.

An ceto jaririyar a raye jim kadan bayan da mahaifiyar mai suna Hauwa Muhammad ta jefa ta a masai, Punch ta ruwaito.

Mai tabin hankali ta jefa jariryarta a masai
Abin Tausayi Yayin da Mata Mai Fama da Tabin Hankali Ta Jefa Jaririyarta a Masai a Jihar Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ya ce:

“A ranar Laraba, 15 ga watan Faburairu, 2023, hukumar kashe gobara ta jiha ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:49 na safe, daga daya daga ma’aikatanmu, Ibrahim Umar Muhammad da ya sanar da faruwar lamarin a Sabon Titi Gidan Kankara a Kano ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

An Gano Wata Kyakkyawar Tsohuwa Mai Shekaru 150 a Najeriya, Bidiyonta Ya Ba Da Mamaki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ma’aikan kwana-kwana sun gaggauta zuwa wurin da misalin karfe 10:54 na safe inda suka tarar da mata mai shekaru 25 mai suna Hauwa Muhammad, wacce aka ce tana da tabin hankali ta jefa diyarta a masai.
“Saboda haka, ‘yan kwana-kwana da suka iso wurin sun shiga aikinsu, sun kuma yi nasarar ceto jaririyar a raye tare da mika ta ga kakanta, Abubakar Umar Usman da ke unguwar Sabon Titi.”

Abdullahi ya kara da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin kafin sanar da al’umma cikakken bayanin yadda abin ya faru, Pulse ta tattaro.

Hukumomin tsaro a Najeriya sun sha ceto irin wadannan yaran daga hallaka bayan samun tsaiko daga iyayensu masu tabin hankali.

Bidiyon yadda budurwa ta nemo tsohon saurayinta da ya haukace a Kano, ta gyara shi tsaf, ta mayar dashi gida

Kara karanta wannan

Kai Mummuna Ne: Budurwa Ta Kunyata Saurayi, Ta Ki Amincewa Ta Aure Shi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

A wani labarin kuma, wata budurwa ‘yan yankin Kudancin Najeriya ta yi tattaki zuwa jihar Kano domin ganin saurayinta da ya zauce, ta dauke shi zuwa garinsu.

A bidiyon da ta yada, ta bayyana yadda take nemansa da kuma yadda ta yi nasarar samunsa a Kano kana ta tabbatar da daukarsa zuwa asalin garinsu domin neman magani.

A cewar budurwar, saurayin nata ya kasance jami’in soja, amma wasu mutane suka yi masa tsafi ya haukace babu gaira babu dalili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel