An Gurfanar Da Abokan Murja Kunya Bisa Yada Batsa Ta Shafin TikTok

An Gurfanar Da Abokan Murja Kunya Bisa Yada Batsa Ta Shafin TikTok

  • Zauren Malaman adidnin Musulunci a jihar Kano sun sake shigar da karar wasu matasa a jihar
  • Ana zargin wadannan matasa ne bisa zargin yunkurin bata tarbiyya ta daura bidiyoyi a kafar sadarwa
  • Alkalin kotun ya tasa keyarsu zuwa gidan gyara hali na tsawon mako daya

Kano - Kotun Shari'ar Musulunci dake Filin Hoki, jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya ta gurfanar da wasu matasan jihar bisa zargin ya'da batsa da rashin tarbiya a manhajar TikTok.

Freedom Radio ta ruwaito cewa wadannan matasa sun hada da Ashir Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya , Aminu BBC da Sadiq Shehu Shariff

Ashir Idris babban aboki ne ga Murja Kunya wacce ita ma ta koma kotu yau, sannan Sadiq Shehu Sharrif wanda ya yi waƙar "A daidai ta nan".

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Ɗan Babban Jigon PDP Har Lahira, Bayanai Sun Fito

Yan Tiktok
An Gurfanar Da Abokan Murja Kunya Bisa Yada Batsa Ta Shafin TikTok Hoto: Freedom Radio
Asali: Facebook

Rahoton ya kara da cewa zauren Malaman Kano ne ya yi ƙarar matasan bisa zargin wallafa bidiyoyin batsa da baɗala a dandalin sada zumunta da watsa bidiyo na TikTok.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ashir Idris dai cikin sauki ya amsa laifinsa.

Sannan Aminu BBC da Sadiq Shehu suka musanta tuhumar da ake musu.

Lauyoyinsu sun bukaci belinsu amma lauyoyin gwamnati suka kiya, sun bukaci a bada mako guda suyi shawara kan haka.

Daga bisani, kotu ta tasa keyarsu zuwa gidan gyara hali zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, 2023.

An Koma Kotu da Murja Kunya yau, Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku

A yau Alhamis, 16 ga watan Febrairu, shahrarriyar yar dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta sake gurfana gaban kotun shari'ar Musulunci dake Filin Hoki jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Arewa Radio ta ruwaito cewa Alkali Mai Shari'a yayi umarni a maida Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali da tarbiyar zuwa mako guda.

Murja dai har ila yau ta musanta tuhumar da ake yi mata a gaban kotu.

Freedom Radio ta ruwaito cewa game da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba.

Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel