NUC Ya Umarci a Rufe Jami'o'in Najeriya Saboda Babban Zaben 2023

NUC Ya Umarci a Rufe Jami'o'in Najeriya Saboda Babban Zaben 2023

  • Hukumar jami'o'i ta tarayya (NUC) ta umarci mahukunta su kulle jami'o'in Najeriya na wani takaitaccen lokaci
  • NUC tace matakin wanda ya hito daga Ministan Ilimi zai ba dalibai damar kaɗa kuri'unsu a babban zaben 2023
  • A cewar hukumar, za'a rufe Jami'o'i ne daga 22 ga watan Fabrairu zuwa ranar 14 ga watan Maris, 2023

Abuja - Hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC) ta umarci a rufe jami'o'i a dukkan sassan ƙasar nan domin baiwa ɗalibai damar ba da gudummuwarsu a babban zaɓen 2023.

Rahoton Punch ya nuna cewa a wata wasika da aka aike wa shugabannin jami'o'i (VC) da Daraktoci, NUC ta bayyana cewa wannan umarnin ya fito ne daga Ministan ilimi, Adamu Adamu.

Hukumar NUC.
NUC Ya Umarci a Rufe Jami'o'in Najeriya Saboda Babban Zaben 2023 Hoto: NUC
Asali: Facebook
"A matsayin shugabannin jami'a (VC) kuna da masaniyar cewa babban zaben 2023 zai gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, na shugaban ƙasa da majalisun tarayya da 1 ga watan Maris, 2023 na gwamna da majalisar dokoki."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mataimakin gwamnan Sokoto ya musanta barin PDP, ya fadi abin da ya faru

"Duba da halin da ake ciki da tsaron ma'aikata, dalibai da kyayyakin makarantu, Ministan ilimi, Mal Adamu Adamu, ya umarci jami'o'i da Cibiyoyin jami'a su tafi hutu tsakanin 22 ga Fabrairu da 14 ga watan Maris, 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda haka, ana umartar VC da daraktoci su rufe makarantunsu daga ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu, 2023 zuwa ranar Talata 14 ga watan Maris, 2023."

- A cewar wasikar da NUC ta aike wa mahukuntan jami'o'i.

Bugu da kari, rahoton Daily Trust yace wasikar ta kara sabunta tabbacin babban Sakataren NUC, Farfesa Rasheed Abubakar, yayin da ya gode wa shugabannin jami'o'i bisa fahimta da kuma haɗin kan da suka bayarwa.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa 'yan Najeriya sun yi ta kiraye-kirayen gwamnati ta ba da hutu a manyan makarantu domin ɗalibai su samu damar kaɗa kuri'a a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu

A bayanan da hukumar zabe ta ƙasa INEC ta fitar, dalibai sama da miliyan 26m ne suka yi rijistar zabe a Najeriya.

Karancin Mai Da Sabbin Naira Ba Zai Hana Yin Zaben 2023 Ba, Shugaban INEC

A wani labarin kuma INEC ta tabbatar da cewa matsalar karancin mai da takardun naira ba zai hana gudanar da babban zabe ba

Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban INEC ta kasa ya ƙara baiwa yan Najeriya tabbacin zabe zai gudana kamar yadda aka tsara a watan Fabrairu da Maris.

Shugaban hukumar ya fito ya bayyana haka ne yayin da ake raɗe-raɗin wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan na da alaƙa da yunkurin hana zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel